Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Neja baya dauke da cutar coronavirus

Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Neja baya dauke da cutar coronavirus

Sakamakon gwaji da aka yiwa gwamnan jahar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya nuna cewar baya dauke da cutar coronavirus.

A ranar Laraba ne dai gwamnan ya shiga killace kansa bayan ya hadu da wasu da aka tabbatar suna dauke da cutar ta covid-19 a taron kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran tarurrukan kasa.

Gwamnan ya kuma bukaci hadimai da yan majalisarsa da su aikata hakan suma.

Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Neja baya dauke da cutar coronavirus
Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan Neja baya dauke da cutar coronavirus
Asali: UGC

A wani jawabi daga babbar sakatariyar labarai ta gwamnan, Misis Mary Noel Berje, gwamnan zai ci gaba da killace kansa duk da cewar baya dauke da cutar domin yin rigakafi.

A cewar sanarwar, gwamnan zai ci gaba da isar da aikinsa daga gida na dan wani lokaci.

Jawabin ya kawo cewa gwamnan ya roki mutane da su rungumin tsaftace kansu, da muhallinsu da kuma sauran matakan da zai kare su daga kwasar mummunan cutar.

“Har yanzu muna kira ga jama’a da kada su tayar da hankalinsu yayinda gwmnati ke daukar matakan hana yaduwar annobar domin jama’a baki daya.”

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

A gefe guda mun ji cewa Kwantrola Janar na hukumar shiga da ficen Najeriya, Muhammad Babandede, ya kamu da cutar Coronavirus. Jaridar Punch ta ruwaito.

Kwantrolan wanda ya bayyana hakan ta silar sakon Whatsapp da safen nan ya bayyana cewa tuni ya killace kansa tun lokacin da ya dawo daga kasar Birtaniya ranar 22 ga Maris.

Yace, “A yau, an tabbatar na kamu da cutar COVID-19. Tuni na killace kaina tun lokacin da na dawo daga kasar Birtaniya ranar Lahadi 22 na watan nan ta jirgin British Airways a Legas.

“Ina kira ga masoyana, jamian hukumar shiga da fice, da yan Najeriya su taimaka min da wadanda suka kamu da addua.”

Ya kara da cewa “Lokacine mai wuya amma ba zamu iya canza abinda Allah ya kaddara mana ba.”

Babandede ya yi kira da ma’aikatansa su cigaba da bada hadin kai ga mataimakinsa domin ciyar da hukumar gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel