Coronavirus: Mutane 2 sun mutu a Afirka ta Kudu a karo na farko

Coronavirus: Mutane 2 sun mutu a Afirka ta Kudu a karo na farko

A yayinda ake ci gaba da kokarin kawo karshen annobar coronavirus da ta addabi duniya baki daya, kasar Afirka ta Kudu ta rasa mutane biyu a karo na farko sakamakon cutar ta covid-19.

Ministan lafiya na kasar, Zwelini Mkhize ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris inda ya kara da cewa mutane biyun da suka mutu duk sun fito ne daga lardin Yammacin Cape, inda daya ya mutu a asibitin kudi yayinda na biyun kuma a asibitin gwamnati.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu yawan mutanen da suka kamu sun wuce 1,000, inda ya ce nan gaba kadan za a bayar da kididdiga.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ta aiwatar da dokar kulle ta kwana 21 a ranar Juma'a domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Coronavirus: Mutane 2 sun mutu a Afirka ta Kudu a karo na farko

Coronavirus: Mutane 2 sun mutu a Afirka ta Kudu a karo na farko
Source: UGC

Tuni dai jami'an tsaron kasar suka fara shawagi don ganin jama'a na martaba dokar rufe kasar da aka dauka ta ba shiga ba fita har tsawon makwanni uku aiwatar da dokar rufe makwanni uku.

KU KARANTA KUMA: Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutum mai suna Emmanuel Benson, wanda ya hadu da wasu mutane biyu da suka dawo daga Ingila a Legas, ya je yayi gwajin cutar COVID-19 kuma an tabbatar masa da yana dauke da ita.

Bayan kammala gwajin a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Idi-Alaba ne aka ce ya koma gida don babu gadon kwantar da shi. Benson wanda ya shirya tsaf don a killacesa sannan a bashi maganin muguwar cutar bayan ya gano yana dauke da ita a ranar 21 ga watan Maris, an bukaci ya koma gida don babu gadon kwantar dashi.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa bayan LUTH ta ki killace Benson, ya koma gida inda ya ci gaba da al'amuransa tare da shiga jama'a yadda ya saba.

"Daga LUTH din ya hau motar haya ne kuma ya ci gaba da mu'amala da jama'a yadda yake yi a baya," wani abokinsa ya sanar da jaridar SaharaReporters a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel