Gwamna Abdullahi Sule ya hana taron biki da haduwar jama'a a Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule ya hana taron biki da haduwar jama'a a Nasarawa

Labari da dumin duminsa da Legit.ng Hausa ke samu daga shafin gidan talabijin na TVC na tuwita (@tvcnewsng) na nuni da cewa gwamnatin jihar Nasarawa a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ta dakatar da taron bukukuwan daurin aure, sauran taron jama'a tare da kayyade taron jama'a zuwa mutum 20.

Kazalika, wuraren ibada za su cigaba da zame a rufe. Za a rufe kasuwanni, wasu 'yan tsirarun 'yan kasuwa ne kawai za a yi wa uzuri su bude shagonninsu domin cinikayya.

A jiya, Laraba, ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa gwamna Abdullahi Sule ya dauki matakin killace kansa tare da cigaba da gudanar da aiki daga gida domin ya rage cudanya da jama’a, don gudun kada ya kamu ko yada cutar coronavirus yayin da ake jiran sakamakon gwajin da aka yi masa, kamar yadda wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta bayyan.

Sanarwar ta kara da cewa: “Idan za’a tuna, Gwamna Sule da kansa ya gayyaci jami’an NCDC zuwa fadar gwamnatin jahar domin su gudanar da gwajin cutar a kansa, amma dukkanin gwaje gwajen da aka gudanar sun nuna baya dauke da ita.

“Za’a cigaba da sanar da jama’a duk wani cigaba da aka samu game da matsayin lafiyar mai girma Gwamna Abdullahi Sule.”

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 9.

Gwamna Abdullahi Sule ya hana taron biki da haduwar jama'a a Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 15,000 a fadin duniya, sannan kuma tana cigaba da mamaya a sassan duniya.

DUBA WANNAN: Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, jimilla 51, ta shiga karin sabbin jihohi 2

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya haura mutum 50 kuma zai iya karuwa, kamar yadda kididdigar da aka yi a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, ta nuna.

Yawacin mutanen da aka samu suna dauke da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

A tsakanin manyan jami'an gwamnatin Najeriya, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa; Abba Kyari, shine na farko da aka fara tabbatarwa yana dauke da kwayar cutar. Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma kakakin majalisar jihar Edo.

Ya zuwa yanzu gwamnoni biyar ne suka killace kansu bayan ta tabbata cewa sun yi cudanya da masu dauke da kwayar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel