Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta fara jigilar tallafin kayan kiwon lafiya da gidauniyar wani attajiri dan kasar China, Jack Ma Foundation, ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar coronavirus.

NAF ta fara jigilar kayan tallafin ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Murtala Mohammed International Airport (MMIA), da ke jihar Legas zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa, Nnamdi Azikiwe International Airport (NMIA), da ke Abuja a ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kayan tallafin sun hada da wasu akwatuna 107 da ke cike da kayan duba lafiya da suka hada kayan tiyata, kayan gano kwayar cutar corona, kayan ma'aikatan lafiya da ke duba marasa lafiya da sauransu.

Bayan isowar kayan tallafin Abuja, NAF ta damka su a hannu wakilan ma'aikatar lafiya a karkashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar, Abdulazeez Mashi Abdullahi, a ranar Laraba, 25 ga watan Maris.

Da yake magana da manema labarai jim kadan baya karbar kayan tallafin, Alhaji Abdullahi ya mika godiya ta musamman ga shugaban rundunar NAF, Air Marshal Sadique Abubakar, bisa jigilar kayan a kan lokaci zuwa Abuja.

DUBA WANNAN: Rudani da firgici a Kano: An hana fasinjoji fita daga jirgi saboda samun marar lafiya

Kazalika, ya mika sakon jinjina ga dukkan sauran dakarun NAF da aka yi amfani da su wajen jigilar kayan. Ya kara da cewa tabbas kayan za su matukar kara wa kokarin gwamnati na shawo kan cutar COVID-19 armashi.

A cikin sanarwar da Air Commodore Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na NAF, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa NAF a shirye take ta bayar da duk wani tallafi ga kasa domin ganin an dakile barazanar da kwayar cutar COVID-19 ke yi wa jama'ar Najeriya.

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Alhaji Abdullahi, babban sakataren ma'aikatar lafiya yayin magana da manema labarai
Asali: Facebook

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Asali: Twitter

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Asali: Twitter

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Asali: UGC

Coronavirus: NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
NAF ta fara jigilar kayan tallafin da attajirin kasar China ya bawa Najeriya
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng