COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwa

COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki babban mataki domin kare yaduwar annobar kwayar cutar coronavirus bayan ta umarci dukkan ma'aikatanta daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida na tsawon kwanaki 30 masu zuwa. Umranin zai fara aiki ne daga ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Kazalika, gwamnatin ta umarci duk wasu 'yan kasuwa su rufe shagunansu. Masu shagon sayar da magani da kayan abinci kadai aka yarda su bude shagunansu a jihar.

A cikin jerin wasu sakonni da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa an yi wa dokar hana jama'a da yawa taruwa a wuri guda biyayya, musamman a coci-coci, masallatai da kuma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ma na addini.

Gwamnan ya shawarci jama'a da su zauna a gidajensu tare da gujewa fitowa waje matukar hakan ba dole ya zama ba, saboda halin da ake ciki na fama da annobar kwayar cutar coronavirus.

COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwa
Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

El-Rufa'i ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da hukumomin tarayya domin sa ido da kuma tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokokin da aka gindaya domin ganin an kare jama'a daga fadawa hatsarin kamuwa da kwayar cutar coronavirus.

DUBA WANNAN: COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta saurara wa wadanda aka samu suna saba umarnin gwamnati ba tare da yin barazanar cewa ba zai yi jinkirin saka dokar ta baci a jihar ba idan bukatar yin hakan ta zama dole.

A cewar El-Rufa'i, tunda coronavirus ta bulla a Abuja, akwai bukatar gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakai masu tsauri domin kiyaye shigowar kwayar cutar cikin jihar da kuma sauran jihohin arewa, musammam yanzu da jama'a ke guduwa daga Abuja saboda tsoron coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel