Gwamnatin Neja ta yi umurnin rufe dukkanin makarantu a fadin jahar saboda coronavirus

Gwamnatin Neja ta yi umurnin rufe dukkanin makarantu a fadin jahar saboda coronavirus

Gwamnatin jahar Neja ta yi umurnin rufe makarantun gwamnati da na kudi da kuma dukkanin makarantun gaba da sakandare a fadin jahar.

Matakin kulle makarantun zai fara aiki daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2020.

Za a rufe makarantun ne na tsawon kwanaki talatin cir.

A wani jawabi daga babban sakataren gwamnatin jahar, Ahmed Ibrahim Matane, akwai bukatar yin hakan a matsayin matakan kare kai daga cutar Coronavirus.

Gwamnatin Neja ta yi umurnin rufe dukkanin makarantu a fadin jahar saboda coronavirus

Gwamnatin Neja ta yi umurnin rufe dukkanin makarantu a fadin jahar saboda coronavirus
Source: Twitter

Ya Kara da cewa yana daga cikin kokarin gwamnati na hana yaduwar annobar Coronavirus da ya karade fadin duniya.

Babban sakataren ya kara da cewa gwamnatin jahar ta dakatar da dukkanin taron jama’a.

Matane ya yi kira ga mutanen jahar da su kula da tsaftar kai sosai, sannan a kwantar da hankali da kuma bin duk wasu matakai na tsare kai kamar yadda ma’aikatar lafiya ta jahar ta sanar.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Kungiyar Ansaruddeen ta dakatar da Sallar Juma'a a masallatanta da ke fadin Najeriya

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa Gwamnonin yankin Arewa maso yamma sun sanar da cewa za a rufe dukkan makarantu da ke yankin na tsawon kwanaki 30 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cikin sakon bayan taro da gwamnonin suka fitar ta bakin shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, sun ce ya zama dole a dauki matakin hakan domin kare yaduwar cutar da Coronavirus a yankin.

An samu samu bullar wata cuta da ake zargin coronavirus ne a jihar ta Katsina a karo na farko a ranar Laraba.

Gwamnonin sun yi taro ne a Kaduna tare da hukumomin tsaro domin yin bita kan tsare-tsaren samar da tsaro a yankin kafin rahoton bullar cutar ya fito a Kaduna a safiyar ranar Laraba.

Gwamna Masari ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

Ya ce gwamnonin za su zauna da hukumomin shirya jarrabawa su tattauna da su kan lamarin.

Sun kuma shawarci al'umma su guji taron mutane idan ba da muhimmin dalili ba kana su cigaba da tsafta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel