Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya kwatanta zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da hannu wajen tube rawanin Muhammadu Sanusi II, da zance mara tushe balle makama.

Idan zamu tuna, a ranar Talata ne dai tsohon gwamnan jihar Kano, Kwankwaso yayi hira da gidan rediyon BBC Hausa. Rabiu Kwankwanso ya zargi hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen tube rawanin Sanusi.

Amma kuma, a martanin gaggawa da Ganduje yayi ta takardar da sakataren yada labarai, Abba Anwar ya fitar, ya ce tube rawanin basaraken hakkin gwamnatin jihar ne kuma hakan ta faru ne saboda gamsassun dalilai.

Kamar yadda gwamnan ya sanar, Sanusi ya take bangare na uku, sashi na 13 na dokokin masarautar jihar Kano din na 2019. Wanda kuwa idan ba a dau matakin gaggawa ba, zai iya bata sunan masarautar Kano din baki daya.

Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari

Sanusi: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari da gwamnan Nasarawa suna ganawa a Aso Rock

“Wannan dokar ta jihar Kano ce ba ta gwamnatin tarayya ba. A don haka ne babu dalilin danganta wannan horarwar da wani sashi da ya wuce gwamnatin jihar.” Ya kalubalanta.

“A don haka ne nake mamakin yadda wani zai fito kwatsam daga wani waje ya fara zargin fadar shugaban kasa da hannu wajen tubr rawanin Muhammadu Sanusi. Dalilan tube masa rawani kuwa a bayyane yake,” Gwamnan ya kara da cewa.

Gwamnan ya kara da jaddada cewa duk wanda ya danganta lamarin da fadar shugaban kasa, toh yana da wata manufa ko kuma kwata-kwata baya son gaskiya.

“Idan ‘yan Najeriya za su tuna, a makon da ya gabata ne shugaban kasa ya bayyana cewa bashi da wata dama wacce kundun tsarin mulki ta bashi na shiga lamarin masarautar jihar Kano din,” Ganduje yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel