Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu

Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu

- Jam'iyyar APC reshen jahar Taraba ya sha alwashin gurfanar da gwamnan jahar, Ishaku Darius wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP a gaban kotu idan har bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ba

- Shugaban jam’iyyar APC a jahar, Ibrahim Elsudi ya bayyana cewa sun bai wa gwamna Darius wa’adin mako guda don ya mika mulkin ga mataimakinsa ko su hadu a kotu

- Sai dai bangaren gwamnan sun yi watsi da barazanar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jahar Taraba ya sha alwashin gurfanar da gwamnan jahar, Ishaku Darius wanda ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a gaban kotu idan har bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ba.

Shugaban jam’iyyar APC a jahar, Ibrahim Elsudi ya bayyana cewa sun bai wa gwamna Darius wa’adin mako guda don ya mika mulkin ga mataimakinsa ko su hadu a kotu.

Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu
Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu
Asali: Depositphotos

Jam’iyyar ta APC na zargin gwamnan jahar da kwashe tsawon watanni biyu ba tare da ya zauna a jaharsa ba, wanda a cewarta ya zarge yawan wa’adin da kundin tsarin kasar ya ba shi.

Sai dai bangaren gwamnan sun yi watsi da barazanar.

KU KARANTA KUMA: Yan watanni da barin Majalisa: Dino Melaye ya fara kukan dawainiya sun masa yawa

A bangare guda, an yi kira ga yan majalisar sokokin jihar Taraba su yi gaggawa tsogi gwamnan jihar, Darius Ishaku, kan kauracewar da yayi jihar tun shekarar 2019.

Watanni biyu cir rabon da gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya taka jiharsa ba kuma mutan jihar sunce yanayin gudanar da aikin gwamnatin jihar Taraba ya ja tsaya cik saboda rashin gwamnan, Rahoton Daily Trust.

Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.

Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba.

Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba.

Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba.

Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel