Saraki: EFCC ba su da hurumin karbe mani gidana a kan an-ce-ka-cen Jama’a

Saraki: EFCC ba su da hurumin karbe mani gidana a kan an-ce-ka-cen Jama’a

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bukaci babban kotun tarayya da ke Legas ta yi fatali da bukatar da hukumar EFCC ta kawo gabanta.

Dr. Bukola Saraki ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta kawo inda ta ke bukatar a karbe gidansa da ke Garin Ilorin a jihar Kwara, a mikawa gwamnatin tarayya.

Bukola Saraki ya fadawa kotu cewa bai kamata ta yi amfani da jita-jitar jama’a da ke cewa an gina wadannan gidaje da dukiyar haramun wajen karbe masa dukiyarsa ba.

Lauyan da ya ke tsayawa Abubakar Bukola Saraki watau Kehinde Ogunwumiju SAN, ya roki kotu ta bukaci Jami'an EFCC su kawo hujjar da ke gaskata zargin da ta ke yi.

Babban Lauyan Bukola Saraki Kehinde Ogunwumiju, ya bayyana cewa akwai bukatar hukumar EFCC ta fito da hujja mai gamsarwa kafin a damka mata gidajen har abada.

KU KARANTA: Gwamnatin Kwara ta rugurguza gidan Mahaifan Bukola Saraki

Saraki: EFCC ba su da hurumin karbe mani gidana a kan an-ce-ka-cen Jama’a
Kotu ta ba EFCC damar karbe wasu gidajen Bukola Saraki a Kwara
Asali: Depositphotos

Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Kwara, ya fadawa Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa cewa EFCC ba su kawo wata hujjar da za ta sa a mallaka masu gidajen ba.

A Dismaban 2019, EFCC ta samu iznin kotu na karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ke Unguwar GRA a Garin Ilorin, da zargin cewa da kudin sata aka gina gidajen.

Haka zalika Saraki ya yi magana ta bakin Mai magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu, wanda ya bayyana cewa ba a filin gwamnati aka gina wadannan gidaje ba.

A cewar EFCC, Saraki ya saci Biliyan 10 daga asusun Kwara a lokacin ya na gwamna, wanda ta ce da wannan kudi aka gina gidajen. Tuni ya karyata wannan zargi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel