Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole

Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya ce babu mai rantsar da dan takarar Jam’iyyar PDP, Sanata Douye Diri a matsayin gwamnan jahar Bayelsa a ranar Juma'a

- Oshiomhole ya bayyana cewa hukuncin kotun koli ya ce a bayar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar da yake da abubuwan da aka bukata a zaben baya ga David Lyon

- Ya ce Diri bai cike bukatun kotun koli ba

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya kaddamar da cewar ba a isa a rantsar da dan takarar Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Douye Diri a matsayin gwamnan jahar Bayelsa ba a ranar Juma’a, 14 ga watan Fabrairu. A cewarsa Diri bai cike bukatun kotun koli ba.

Oshiomhole ya bayyana cewa hukuncin kotun koli ya ce a bayar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar da yake da abubuwan da aka bukata a zaben baya ga David Lyon.

Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole
Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole
Asali: UGC

Ya ce babu wani dan takara a zaben da ya cike abubuwan da aka bukata a zaben illa Lyon, inda ya kara da cewa abun da ke ciki shine daga ranar Juma’a Bayelsa za ta kasance ba tare da Gwamna ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

A baya mun ji cewa Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerar zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon da kuma abokin tafiyarsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, wadanda suke ta shirye-shiryen karbar rantsuwar hayewa karagar mulkin jihar.

Alkalai biyar na kotun, wadanda suka samu shugabancin Mai shari'a Mary Peter-Odili, sun umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye shahadar hayewa kujerar jagorancin jihar da ta mikawa 'yan takarar jam'iyyar APC din a jihar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Duba da wannan kalami kuwa, jam'iyyar PDP ce za ta amshe wannan kujerar don ci gaba da mulkin jihar ta Bayelsa.

Mai shari'a Ejembi Ekwo, wanda ya karanto hukuncin kotun kolin, ya bada wannan umarnin ne bayan da aka bayyana rashin cancantar mataimakin David Lyon, Degi-Eremienyo a tsayawa takarar zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel