An tsinci gawar saurayi da budurwa a dakin janerato a unguwar Badawa a Kano

An tsinci gawar saurayi da budurwa a dakin janerato a unguwar Badawa a Kano

Wani mutum mai suna Auwallu Abdullahi mai shekaru 25 da budurwasa mai shekaru 19 an tsinci gawarsu a dakin janareto a Unguwar Gaya da ke yankin Badawa a cikin birnin Kano.

Ana zargin masoyan biyu sun mutu ne sakamakon hayakin janareton bayan sun kulle kansu a dakin Janareton na dogon lokaci. Lamarin ya faru ne wajen karfe 9 na dare a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiya ta sanar da jaridar Daily Trust cewa wata matar aure ce ta gano gawawwakin a dakin Janareton da ke gidan.

An ce matar ta hanzarta sanar wa 'yan sanda wadanda suka hanzarta mika masoyan asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsu.

An tsinci gawar saurayi da budurwa a dakin janerato a unguwar Badawa a Kano
An tsinci gawar saurayi da budurwa a dakin janerato a unguwar Badawa a Kano
Asali: Original

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hukumar sun samu labarin ne wajen karfe 9:30 na daren Laraba. Ya ce jami'an sun hanzarta zuwa wajen inda suka kwashesu zuwa asibitin kwararru na Murtala. A nan ne aka tabbatar da mutuwar dukkansu biyun.

DUBA WANNAN: Abinda Abdulmumin Kofa ya fada a Kan Ganduje bayan ya ziyarce shi (Hotuna)

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Habu A. Sani, ya bada umarnin tsananta bincike don gano yadda wannan abin mamakin ya faru.

Wata majiya wacce ba mai karfi ba ta tabbatar da cewa Auwallu Abdullahi da budurwarsa na kokarin yin aure ne kafin aukuwar mummunan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel