Lai Mohammed ya ce Najeriya ta fi kowace kasa ‘Yanci da tsaro

Lai Mohammed ya ce Najeriya ta fi kowace kasa ‘Yanci da tsaro

Lai Mohammed ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta yi watsi da dokokin kasa da hakkin jama’a wajen kawo wasu sababbin kudiri ba.

Yanzu haka akwai wasu kudirori a majalisa da su ke neman hana kalaman kiyayya da kuma sa ido wajen yadda ake amfani da dandalin sadarwan zamani.

Mohammed wanda shi ne Ministan yada labarai da al’adu ya ce babu ta inda wadannan kudirori su ka ci karo hakkin da doka ta yi wa ‘Yan Najeriya tanadi.

Duk da rashin tsaron da ake fama da shi a yanzu, Ministan ya fito gaban Duniya ya na bayyana cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowace aminci a kaf Duniya.

KU KARANTA: Buhari ya dauki mataki game da matsalar rashin tsaro

Lai Mohammed ya ce Najeriya ta fi kowace kasa ‘Yanci da tsaro
Alhaji Lai Mohammed ya ce Najeriya ta fi ko ina dadin zama
Asali: Facebook

Alhaji Lai Mohammed ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan kasar Finland a Najeriya, Dr. Jyrki Pulkkimen inji Jaridar nan ta Pulse.ng.

Dr. Jyrki Pulkkimen da Tawagarsa sun kawowa Ministan tarayyar ziyara ta musamman ne a ofishinsa da ke Abuja a Ranar Litinin, 3 ga Watan Fubrairun 2020.

A dalilin wannan zama da Jakadan Finland ne har gwamnatin Najeriya ta fara shirin kiran taro na masu ruwa da tsaki wajen sha’anin dandalin yada zumunta.

Kudirorin da ke gaban majalisar tarayya za su kawo gyara ne a shafun sada zumunta, sannan kuma su kawar da yada kalaman batanci, a cewar Ministan kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel