Jam’iyyar PDP reshen Kano ta ce ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya

Jam’iyyar PDP reshen Kano ta ce ta amince da hukuncin kotun koli da zuciya daya

Biyo bayan nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ya kaddamar da cewar sun karbi hukuncin kotun koli da zuciya daya.

“Mun gode ma Allah madaukakin sarki akan halin da ake ciki a yanzu. Kamar yadda kuka sani mun ji babbar kotu inda hukuncin bai yi mana ba sannan muka daukaka kara, anan ma bamu yi nasara ba. Don haka sai muka dauki mataki guda na karshe sannan muka je kotun koli.

“Mun karbi hukuncin karshe sannan za mu cigaba da kokari don inganta jam’iyyarmu,” in ji shi.

Shugaban PDP din ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu sannan su tabbatar da ganin cewa ba su shiga kowani rikici ba.

Ya ce: “Kirana ga magoya bayanmu shine su kwantar da hankalinsu kan halin da ake ciki. Mu zo mu hada hannu domin inganta jam’iyyarmu zuwa gaba.”

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Zabukan gwamna: An janye Shugaban alkalan Najeriya daga kwamitin kotun koli

A halin da ake ciki, mun ji cewa garin Kano a ranar Litinin ya cika da murna tare da farin ciki bayan kotun koli ta jaddada nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben ranar 9 ga watan Maris 2019.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa miliyoyin jama'ar jihar sun fito daga gidajensu don nuna murnarsu bisa ga nasarar Ganduje duk da sanyin da garin ke ciki. A hankali kuwa jama'a suke komawa kan harkokinsu na yau da kullum a fadain jihar.

A yayin martani ga nasarar Ganduje, Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya ce ikon Allah ne da kuma burin mutane suka tabbata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel