Nayi aure ne a kasar Thailand shine yasa na bar Kannywood - Rashida Labbo

Nayi aure ne a kasar Thailand shine yasa na bar Kannywood - Rashida Labbo

- Tsohuwar jarumar Kannywood mai suna Rashida Lobbo ta ce aure tayi shiyasa ba a ganinta a fina-finai

- Kamar yadda ta bayyana, tana zaune ne a kasar Thailand a cikin birnin Bangkok tare da mijinta dan asalin kasar Mali

- Jarumar tace ta boye aurenta ne don wannan rayuwarta kadai ta shafa

Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa mai suna Rashida Lobbo ta zanta da fim magazine bayan da tayi shekara daya ba a ji duriyarta ba a masana'antar.

Amma kuma bayan rashin ganinta, Rashida na wallafa hotunanta a shafukanta na sada zumuntar zamani a kasar Thailand.

Kamar yadda tsohuwar jarumar ta bayyana, ita haifaffar kasar Kamaru ce kuma tayi karatu a Najeriya inda ta zauna da 'yan uwanta a Abuja. Rashin cikar burinta na zama ma'aikaciyar gidan talabijin yasa ta fada harkar fim. Tayi fina-finan Hausa da na turanci a masana'antar Nollywood.

A zantawar da aka yi da Rashida, ta bayyana cewa tayi aurene kuma suna zama tare da mijinta mai suna Abubakar dan asalin kasar Mali, a birnin Bangkok dake Thailand.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Nnamdi Kanu ya bayyana kudurinsa na bawa Amotekun mutane miliyan 1

Jarumar tace sana'ar mijinta siyar da gwal kuma yayi shekaru 26 a kasar Thailand.

Kamar yadda Mujallar Fim ta 'Fim Magazine' ta bayyana, Rashida ta ce tana matukar kewar abokan aikinta na masana'antar fim kuma tana kewar mahaifiyarta don tun a 2018 da tayi aure bata sake zuwa Najeriya ba.

Da aka tambayeta dalilin da yasa ta bar masana'antar kuma tayi aure a sirrance, jarumar ta ce saboda lamarin rayuwarta kadai ya shafa. Tana jin harshen faransanci ne saboda mahaifiyarta na kasar Kamaru kuma tana zuwa hutu. Harshen turanci kuwa tana jinshi ne saboda karatun da tayi a Najeriya.

Ta bukaci addu'a daga masoyanta tare da fatan zaman lafiya da zuri'a ta gari, don har yanzu bata haihu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng