Manyan ayyuka 12 da gwamnatin Buhari za ta kammala a 2020 – Shugaban kasa ya tabbatar

Manyan ayyuka 12 da gwamnatin Buhari za ta kammala a 2020 – Shugaban kasa ya tabbatar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Labara, 1 ga watan Janairu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kammala manyan ayyuka 12 a 2020.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabin kasa, wanda Legit.ng ta samu cikakken jawabin.

A jawabin, shugaban kasar ya kuma ambaci nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan fara mulkinsa.

Ya kuma yi alkawarin cewa ba zai nemi tsawaita wa'ain mulkinsa ba idan wa'adin shugabancinsa na biyu ya kare a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Ga jerin manyan ayyuka 12 da shugaban kasar ya ce za su kammala:

1. Tituna 47 da za a yi a tsakanin 2020/21 da suka hada da hanyoyin da suka dangana zuwa ga tashoshin ruwa.

2. Manyan gadoji musamman gadar Second Niger Bridge.

3.Kammala ayyukan rukunin gidaje 13 karkashin tsarin samar da gidaje na kasa.

4. Kaddamar da filayen jirgin Lagos da Kano da Maiduguri da Enugu a 2020.

5. Kaddamar da shirin aikin gona a karkara a kananan hukumomi 700 a tsawon shekaru uku.

6. Kaddamar da shirin gandun kiwon dabbobi a Gombe.

7. Horas da ma'aikata 50,000 domin taimaka wa malaman gona 7,000 da ake da su.

8. Kaddamar da tiitn jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri a watanni ukun farkon 2020.

9. Fara aikin hanyar jirgin kasa da za ta tashi daga Ibadan zuwa Abuja da kuma Kano zuwa Kaduna a farkon watannin ukun 2020.

10. Kara sakar wa harkar wutar lantarki mara domin bai wa masu sanya hannun jari damar samo da sayar da wutar lantarki.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta tabbatar da janye jakadu shugabannin hukumomin waje 25

11. Fara aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilla a watannin shidan farkon 2020.

12. Fara aikin jan bututun iskar gas AKK gas pipeline, da OB3 gas pipeline da kuma fadada bututun iskar gas din na Escravos zuwa Lagos a watanni ukun farko na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel