Gwamnatin tarayya ta tabbatar da janye jakadu shugabannin hukumomin waje 25

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da janye jakadu shugabannin hukumomin waje 25

- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sallamar jakadu da shugabannin hukumomin waje 25

- Hakan ya biyo bayan turjiya da aka samu daga jakadun da lamarin ya shafa wadanda suka ce wa’adin Disamba 31, 2019 da aka basu ya yi kusa da yawa

- Jakadun da shugabannin hukumomin dai sun nemi a kara masu watanni biyu zuwa uku domin su kammala wasu ayyukan diflomasiyya kafin janye su

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da janye jakadu da shugabannin hukumomin waje su guda 25.

Tabbatarwar ya biyo bayan turjiya da aka samu daga jakadun da lamarin ya shafa wadanda suka ce wa’adin Disamba 31, 2019 da aka basu ya yi kusa da yawa.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya aika wa jakadun rubutacciyar wasika a watan Nuwamba, inda ya yi umurnin cewa su dawo Najeriya a ranar ko kafin 31 ga watan Disamba.

Ya kuma tunatar masu da lokacin ritaya na Disamba 2018 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin.

Amma jakadun da shugabannin hukumomin sun nemi a kara masu watanni biyu zuwa uku domin su kammala wasu ayyukan diflomasiyya kafin janye su.

Jakadun na bukatar lokaci su hada kayayyakinsu da kuma kai ziyarar bankwana ga shugabannin kasashen da suke kamar yadda yake a tsarin gudanarwar diflomasiyya.

Da yake martani ga matsayar jakadun, kakakin ma’aikatar, Ferdinand Nwonye, ya ce babu wata matsala kan kiranyen.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah ku dinga sanya mu a hanya idan munyi abinda ba daidai ba - Sanata Ahmad Lawan ya roki 'yan Najeriya

Nwonye a jawabin baya yace neman karin da jakadu da shugabannin hukumar ke yi ya kasance son zuciya, cewa kai tsaye wasikar da aikawa jakadun ya tsige su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel