An horas da ni a kan yadda zan tagayyara makiyi na – Bello El-Rufai

An horas da ni a kan yadda zan tagayyara makiyi na – Bello El-Rufai

Babban dan gwamnan jahar Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana cewa tarbiyyar daya samu a gida ita ce kada ya saurara ma duk wani makiyinsa ko kuma duk wani mai adawa da shi.

Jaridar The Cables ta ruwaito Bello ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani ga wasu ma’abota shafin kafar sadarwar zamani ta Twitter, da suka ayyana bambamcin ra’ayi da Bellon game da rahoton kama Sanata Shehu Sani da EFCC ta yi.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga jahar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya

An horas da ni a kan yadda zan tagayyara makiyi na – Bello El-Rufai
An horas da ni a kan yadda zan tagayyara makiyi na – Bello El-Rufai
Asali: Twitter

A ranar Talata, 31 ga wata Disamba ne hukumar EFCC ta yi ram da Sanata Shehu Sani bisa tuhumarsa da take yi da damfarar wani hamshakin attajiri a garin Kaduna, Alha Sani Dauda ASD Motors, da sunan zai hada shi da shugaban EFCC Ibrahim Magu.

Da yake tsokaci game da rahoton, Bello yace: “Rahotanni sun nuna EFCC ta kama tsohon Sanata kwamared Shehu Sani a kan zarginsa da aikata zamba. Wannan ya nuna duk wani yaudara yana da iyaka.”

Sai dai wani ma’abocin Twitter mai suna Peter Adepoju yace masa: “Na san zaka yi farin ciki da wannan labari fiye da kowa.” Nan da nan Bello ya amsa masa da cewa: “An horas da ni ne a kan yadda zan lalata makiyina gaba daya.”

Sai dai daga bisani Bello ya koma shafinsa na Twitter ya goge rubutun. Sanin kowa ne cewa mahafin Bello, gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai da Sanata Shehu Sani basa ga maciji da juna tun bayan darewarsa kujerar gwamna.

Wannan rikici ya yi kamari da har ta kai ga gwamnan ya zabo hadiminsa, Uba Sani domin tsayawa takarar kujerar Sanatan Kadun ta tsakiya, hakan ta sanya Shehu Sani ficewa daga APC, daga karshe Uba Sani ya samu nasara, a yanzu dai Bello hadimin Uba Sani ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel