An haramtawa Maza da Mata haduwa cikin dare a wani Gari a Jigawa

An haramtawa Maza da Mata haduwa cikin dare a wani Gari a Jigawa

Karamar hukumar Kirikasamma a ke jihar Jigawa, a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, ta sanya dokar dake haramtawa jinsi mabanbanta haduwa da daddare.

Karamar hukumar ta bayyana hakan ne sakamakon yawan samun cikin shege a tsakanin yan mata.

Jami’in labarai na karamar hukumar, Sanusi Doro ya ce Shugaban karamar hukumar, Salisu Kubayo, ya sanya hannu a dokar bayan kansilolin karamar hukumar 10 sun amince a hakan a lokacin wata ganawa.

A cewar sabon dokar, daga yanzu, duk mace da namiji da aka samu da karya dokar koda masoya ne za su fuskanci hukuncin daurin watanni shida a gidan yari tare da zabin biyan N50,000 a matsayin tara.

Mista Doro ya ce masoya na gaskiya na iya haduwa ne kawai a rana don tattaunawa. An sanya hannu a okar ne a wani budadden taro da ya samu halartan mazauna Yankin ciki harda babban limamin garin.

Haka zalika, Shugaban kansilolin karamar hukumar, Sa’iu Marma, ya ce akwai bukatar sanya dokar biyo bayan yawan korafin da ake samu daga iyaye game da lamarin yin cikin shege sakamakon haduwa da ake yi tsakanin mata da maza domin tattaunawa da kuma haduwar dare.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta bayyana dalilin da yasa motar yakinta ya babbake a Damaturu

Mista Marma ya kara da cewa a matsayinsu na shugabannin su za a rike idan aka samu nasara ko akasin haka a yankin. Ya ce zina da cikin shige a tsakanin mata ya zama babban kalubale da yankin ke fuskanta wanda hakan ya sa aka kafa dokar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel