Zamfara: Yari ya rika satar albashin Ma’aikatan bogi 4, 972 - Kwamishina

Zamfara: Yari ya rika satar albashin Ma’aikatan bogi 4, 972 - Kwamishina

Sabon Kwamishinan kudin jihar Zamfara, Rabiu Garba-Gusau, ya bankado cewa tsohon gwamna Abdulazeez Yari ya kirkiro Ma’aikatan karya 4, 972, wanda ake ware masu albashi.

A duk wata gwamna Abdulazeez Yari ya na samun Naira miliyan 216 a duk wata kamar yadda Kwamishinan harkar kudin ya bayyana a lokacin da ya yi hira da Manema labarai

“Ma’aikata ne wadanda ba su cikin jerin ainihin ma’aikatan jihar amma sun samu daurin-gindin shiga cikin masu daukar albashi a ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati.”

A cewar Kwamishinan, akwai ma’aikata 1640 da lambar asusun bankinsu ba ya cikin uwar-garken ma’aikata da wasu 119 da aka samu banbanci wajen lambar asusun bankinsu.

KU KARANTA: Wadanda rigimar Sanusi II da Ganduje ta ci a Masarautar Kano

“A maimakon lambar asusun banki, an yi amfani da lambobi masu kama da na wayar salula aka yi amfani da su, amma kuma a karshen rana kuma kudi ya na shiga asusun bankinsu.”

“Mun dakatar da biyan wannan albashi, kuma binciken mu zai cigaba saboda kokarin ganin ba a wawurar dukiyar jihar Zamfara.” Jaridar nan ta Daily Nigerian ta rahoto wannan labari.

Garba-Gusau ya bayyana cewa Mukhtar Shehu-Idris (watau Kogunan Gusau) wanda ya rike Kwamishinan kudi a gwamnatin APC shi ne ya kitsa wannan danyen aiki da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel