Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya haramta wa Sokon Kano, Alhaji Ahmadu Abdulwahab shiga fada. Wannan matakin ya biyo baya ne, kasa da sa'o'i 24 bayan kwamitin sasancin da ya samu shugabancin tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdussalami Abubakar, ya roki Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi da su gujewa daukar wani mataki da ke da alaka da kirkirar sabbin masarautun jihar.

An gano cewa, Sokon Kano ya yi wasu kalaman kaskanci ne ga Sarkin a yayin da suka halarci yaye hafsoshin 'yan sanda a jami'arsu dake Wudil. A wani bidiyo da ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani, an ga Sokon Kanon yana kalaman a yayin bikin yayen 'yan sandan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A yayin tabbatar da ci gaban, jaridar Daily Trust ta kira Sokon Kano a wayar tafi da gidanka don zantawa dashi. Kamar yadda ya ce, "Na isa fadar a safiyar Litinin. Na shiga cikin sauran abokan aikina don raka Sarkin zuwa fada. Amma mintoci kadan bayan isarsa kan karagarsa, shugaban ma'aikatan fadar, Alhaji Munir Sanusi ya isko ni."

DUBA WANNAN: Me ya yi zafi? Babban dan sanda ya harbe dan uwan aikinsa, ya kashe kansa a take

"Ya tambayeni dalilin da yasa nazo fada, kuma na sanar dashi cewa aikina nake yi. A take ya sanar dani cewa ba a bukatar sake gani na a fadar saboda ba zai yuwu in hada kai da makiyan fadar ba kuma a lokaci daya ina tare da Sarkin." in ji Sokon Kano.

"A take ya bukace ni da in bar fadar kuma kada in sake komawa. A yayin da nake zaune, ya kira shugaban dogaran fadar. Bayan tattaunawar mintoci tare da shi, sai ya bukace ni da in bar fadar," in ji shi.

A halin yanzu, Sokon Kano ne mutum na uku da Sarki Sanusi ya kora daga fadar sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninsa da Ganduje. Na farko shine sakataren sarkin, Alhaji Isa Pilot, mai biye dashi shine Majasirdin Kano, Alhaji Auwalu Idi.

Duk kokarin samun zantawa da shugaban ma'aikatan sarkin, Munir Sanusi da aka yi, hakan bai samu ba saboda ba ya daukar wayarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel