Gasar haddar Qur'ani ta duniya: Matashi dan kasar Amurka ya kafa tarihi

Gasar haddar Qur'ani ta duniya: Matashi dan kasar Amurka ya kafa tarihi

- Gasar haddar Qur'ani mai girma ta duniya da aka yi a Dubai ta wannan shekarar ta zo da abun mamaki

- Ahmed Burhan Mohammed dan asalin Minnesota dake Amurka mai shekaru 17 ne ya lashe gasar

- Ahmed ya karanto daga surori daban-daban da ayoyi na Qur'ani mai girma kuma ya lashe gasar

Gasar haddar Qur'ani mai girma ta duniya ta shekarar nan ta cika da abubuwan mamaki. Hakzalika, an kafa babban tarihi don an samu wani matashi mai shekaru 17 a duniya da ya lashe gasar, kamar yadda jaridar Mvslimfeed ta ruwaito.

Ahmed Burhan Mohammed dan asalin Minnesota ne daga kasar Amurka. Shi ne matashin da yayi nasarar cin gasar haddar Qur'ani ta duniya, inda ya bige masu gasa sama da 100 daga kasashe daban-daban na duniya. Ahmed ya zama zakaran gwajin dafi don ya bige manyan mahaddatan duniya.

DUBA WANNAN: Kallabi tsakanin rawuna: Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma'aikatan jiha

Ahmed dan asalin kasar Amurka ne amma tsatsonsa daga kasar Somali ne. Mazaunin tsakar birnin Minnea ne, birnin da ya kunshi mutanen kasar Somali.

Shugaban kasar Somali ya bayyana bukatarsa ta haduwa da Ahmed bayan da ya ci gasar da ke da matukar martaba a idon duniya.

Ahmed ya samu maki mafi yawa daga karatunsa, muryarsa da kuma kira'arsa. Ya karanto daga surori daban-daban da ayoyi wadanda ya haddace daga Qur'ani mai girma. Ahmed ya samu kyautar $68,000 da kuma kambun girmamawa. A halin yanzu yana fatan shiga irin gasar kuma ya kara yin nasara.

Ahmed ya samu horarwar karatunsa ne daga wata makarantar Islamiya dake kusa da gida. Ya sadaukar da nasararsa ga iyayensa da malamansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel