Tirkashi: Wata mata ta gano yadda aminiyarta da suka shekara 25 suna tare ta aure mata miji

Tirkashi: Wata mata ta gano yadda aminiyarta da suka shekara 25 suna tare ta aure mata miji

- Wata mata ta wallafa babban labari na yaudara da cin amana da ta taba gani a rayuwa

- Aminiyar shekaru 25 ce ta shiga ta fita, tasa mijin kawa ya saketa tare da aureshi

- Rukevwe da Cordelia kawaye ne kuma aminan juna na sosai amma ashe ba da zuciya daya ake tare ba

Wata mata ta shiga tsananin mamaki a rayuwarta bayan da ta gano cewa mijinta ya auri aminiyarta ta shekaru 25.

Wata ma’abociyar amfani da kafar sada zumuntar Facebook mai suna Christine Aluyi, wacce ta san duk matan fiye da shekaru goma a tare, ta wallafa wannan labarin.

Christine ta bayyana cewa, aminan juna biyu masu suna Rukevwe da Cordelia sun kasance kawaye ne sama da shekaru 25 tare. Rukevwe tayi aure, amma daga baya sai suka rabu da mijin bayan da take da ‘da daya. A bangaren Cordelia kuwa, tayi aure kuma tana zaune lafiya. Gidanta dake Warri tamkar gidan Rukevwe ne.

Bayan shekaru 10, Cordelia da maigidanta sun koma UK kuma a kowanne lokaci suna maraba da zuwan Rukevwe ziyara. Aminan junan suna da wata kawa mai suna Bawo amma tayi aure kuma ta mayar da hankali a kan iyalanta.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kashe ango da duka a lokacin da ake tsaka da shagalin bikinsa

A watan Yuli na wannan shekarar, mai gidan Cordelia ya matsa mata a kan saki, wanda daga baya ta amince kuma ta cigaba da rayuwarta.

Daga baya sai ta shirya tsaf don dawowa Najeriya amma da bukatar zama tare da Rukevwe a gidanta. Amma sai Rukevwe ta nuna rashin amincewarta.

Cordelia ta dawo Najeriya inda ta sha mamaki. Ta tarar da cewa, aminiyarta Rukevwe na gudunta ne don ta aure mata miji. A takaice kuwa, Rukevwe ce ta tirsasa mijin Cordelia rabuwa da ita kuma ya aureta.

“Babbar cin amanar wannan karnin da na taba gani. Ubangiji ya karemu da makiya a matsayin abokai,” Christine ta wallafa a karshen labarinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel