Wani bakatsine ya sauya sunansa daga Buhari zuwa Sulaiman

Wani bakatsine ya sauya sunansa daga Buhari zuwa Sulaiman

- Wani bawan Allah mazaunin Dustin-Ma ya shirya tsaf don sauya sunasa daga Buhari zuwa Sulaiman

- Mutumin ya yanke hukuncin sauyin sunan ne bayan da ya zargi gwamnatin shigaba Buhari da yaudara

- Za a yi bikin radin sunan ne a ranar 14 ga watan Disamba na wannan shekarar, kafin ya shirya sauya na jaririnsa mai suna Buhari

Wani bawan Allah mazaunin karamar hukumar Dutsin-ma a jihar Katsina, ya sanya ranar radin sunansa bayan ya sauya daga Buhari zuwa Sulaiman.

Mutumin ya yi hakan ne bayan da ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari da jefa shi cikin mawuyacin hali. Ya zargi gwamnatin da yaudarar kasar nan baki daya.

Buhari ya ce: "Bana son a ringa kirana da Buhari, saboda yaudara ta gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari."

DUBA WANNAN: Neman mafita: Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da muhimmin taro a Kaduna

Wani bawan Allah mazaunin Dutsin-ma a jihar Katsina ya sanya ranar radin sunansa bayan ya sauya daga Buhari zuwa Sulaiman.

Mutumin ya yi hakan ne bayan ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari da jefa cikin mawuyacin hali. Ya zargi gwamnatin da yaudarar kasar nan baki daya.

Amm kuma cikin makon da ya gabata ne, wani mutum a jihar Kano ya sauya sunansa zuwa Buhari. A shirin shagalin bikin radin sunan ne, ya buga harda katin gayyata. Wannan katin kuwa ya zagaye kafafen sada zumuntar zamani, lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel