‘Yan Acaba: AYCF ta na yi wa Gwamnatin Legas barazanar zuwa gaban kotu

‘Yan Acaba: AYCF ta na yi wa Gwamnatin Legas barazanar zuwa gaban kotu

Ahmed Yerima, wanda shi ne shugaban kungiyar nan ta Matasan Arewa mai suna Arewa Youths Consultative Forum, ya jawo hankalin jama’a cewa ana kama ‘Yan Arewa da ke Acaba a Legas.

Alhaji Ahmed Yerima ya bayyanawa Duniya cewa Jami’an tsaro su na kamen Bayin Allah da ke tukin babur na kudi watau Okada. Mafi yawancin masu wannan sana’a mutanen yankin Arewa ne.

Yerima ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wata zantawa ta musamman da Legit.ng kwanan nan. Alhaji Yerima ya nuna cewa za su kalulabalanci abin da gwamnatin Legas ta ke yi, a kotu.

“Mun shigo Gari kwanaki biyu da su ka wuce, tun kafin nan dama, labari ya na samu na a Kaduna cewa wasu abubuwa su na faruwa a Legas. Akwai wasu jami’an sintiri da ke aiki a cikin jihar Legas.”

KU KARANTA: Wani Matashi da ya rika wajen garkuwa da mutane ya shiga hannu

Yarima ya cigaba da bayyanawa Legit.ng cewa: “Abin da su ke yi shi ne, tsakanin karfe 1 zuwa 2, sai su kutsa gidaje, ka da ku manta, fiye da 80% ko 85% na ‘Yan Acaba daga Arewa su ka fito.

“Abin da su ke yi shi ne, sai su samu wani wuri da ake ajiye daruruwan babura, su shiga. Ban san inda Legas ta yin dokar da ta haramta aikin Acaba a wasu wurare ba.” Inji Shugaban na AYCF

“Ta ya za ka iya yi mani bayanin yadda za ka shiga hurumin wani, ka saba doka da jami’an tsaro da tsageru.” Yarima ya tambaya, ya kara da cewa har jami’an tsaro su kan yi wannan aiki.

A wani jawabi da ya shigo hannunmu a Ranar Litinin 9 ga Watan Disamban 2019, wanda Yerima Shettima ya sa wa hannu, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel