A matse nake in yi aure - Jaruma Saima Muhammad

A matse nake in yi aure - Jaruma Saima Muhammad

Fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood, Saiam Muhammada ta ce ko gobe ta samu mijin aure, za ta shiga daga ciki. Jarumar ta dade tana jan zarenta a masana'antar, duk da cewa ba kowane irin fim take fitowa ba, kasancewar ta ce sai ta zabi fim din da zai koyar da mutane abin kirki.

Ga wadanda suka san jarumar, sun san irin rawar da ta taka a masana'antar. Hakazalika an daina jin duriyarta. Jarumar ta ce, ta dau hutu ne don ganin an samu suaye-sauye a yanayin fina-finan masana'antar.

A cikin fina-finan da jarumar ta taka rawar gani kuma ya yi fice akwai fim din Zuri'a. Jarumar ta fito a matsayin matar Ali Nuhu, daga baya ta kamu da cutar sankarar non, wadda saboda hakan ta umarci maigidanta da ya auro Zainab Indomie. Da knat ta rika rokon Zainab Indomies din da ta auri mijinta saboda muguwar cutar da take dauke da ita. Daga bisani sai ta amince don aurenshi.

DUBA WANNAN: Mu masu gyaran tarbiya ne - Teema Makamashi

A wata hira da Saima ta yi da BBC, ta bayyana cewa ta shiga Masana’antar Kannywood ce domin son ci gaba da kuma kokarin yin wani abu mai kyau da mutane za su rika tunawa da ita.

Sannan ta ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, inda ta ce tana fata Allah Ya kawo mata miji.

Na shiga masana’antar ce saboda ina son ci gaba, ina son yin wani hobbasa mai kyau da mutane za su gani su yi koyi da mu. Ko lokacin da na fara, idan ka kawo min labarin fim, idan na ga shirme ya fi yawa sai in ce ba zan yi ba. Ko a baya-bayan nan, an rika magana a kan an cika waka da sauransu. Sai na dauki hutu in je in dawo, watakila idan na ga abin ya yi min sai in ci gaba.

“Har na je Kaduna na yi fim guda daya, amma kamar yadda na fada sai na zabi fim da nake so. A zo a ce kawai an kawo wane ne mijina, za mu fito mu yi ta rawa muna waka. Ba zan karbi wannan ba. Zan karbi wanda zai koyar da mutane wani abu ne. Daga nan sai na yi aure, na auri wani dan asalin kasar Kongo Brazabille, amma mun rabu.”

Game da sake aure Saima ta ce, “Aure rai ne da shi. Allah ne Ya halicci aure, Ya halicci saki duk da cewa ba Ya son saki. Dole sai an yi hakuri domin zama da mijin yanzu. Duniya ce ta zo karshe, ba wai ’yan Kannywood ba ne kawai. Amma da yake mun fito da kanmu duniya, shi ya sa ake ganinmu. Amma ba a kanmu ba ne kawai.

A taya ni da adu’a, a matse nake in yi aure. Ko gobe na samu miji zan yi aure,” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel