Na ji dadi da Kamfanin NITEL ta mutu – Inji Gwamna El-Rufai

Na ji dadi da Kamfanin NITEL ta mutu – Inji Gwamna El-Rufai

A karshen makon da ya shude, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa tsohon kamfanin sadarwa, NITEL ya batar da Dala biliyan 7 na dukiyar ‘yan kasar nan a banza.

Mai girma gwamnan ya bayyana cewa kamfanin na NITEL ya barnatar da wannan makudan dukiya ne a karon banza. Nasir El-Rufai ya yi wannan jawabi ne Ranar Lahadin nan a Legas.

Malam Nasir El-Rufai ya ke cewa ya ji dadi da kamfanin sadarwar kasar a lokacin, ya mutu. El-Rufai ya ce kamfanin ya gawurta amma ta kai bai iya kirkirar komai, don haka ya mace a sannu.

Gwamna na Kaduna ya bayyana cewa kamfanin NITEL bai taimaki Najeriya a daidai lokacin da ake da matukar bukata ba. El-Rufa ya ce: “Na ji dadi da NITEL ya mutu. Ya cancanci ya mutu.”

El-Rufai ya kafa hujja ne da cewa kamfanin ya kasance ya na kawowa Najeriya ci-baya. “(NITEL) ya da dakile cigaban Najeriya. Kamfanonin sadarwan da su ka fito sun mamayesu.” Inji shi.

KU KARANTA: Gidajen da su ka fi kowane kyau a duk Najeriya

Shekaru fiye da goma da su ka wuce, aka samu wani irin juyi a kasar nan, inda kamfanonin sadarwa su ka shigo. Wadannan kamfanoni sun yi galaba a kan kamfanin gida na NITEL.

El-Rufai ya ce duk da kudin da gwamnati ta kashe a kan kamfanin, layukan tarho 450, 000 aka yi samarwa kaf mutanen Najeriya, duk da haka kuma farashin wayarsu ya na da ‘dan karen tsada.

Gwamnan ya ce NITEL sun yi ba-ba-kere a harkar sadarwa a baya, sannan kuma sun hana hukumar NCC yin aiki, ya ce wani Ministan Abacha ne ya fara tunanin shigo da kamfanonin waje

Tsohon shugaban hukumar BPE mai alhakin kula da kadarorin gwamnatin tarayya ya yi duk wannan jawabi ne a wajen taron bikin da aka shirya domin murnar cikar ALTON shekaru 20.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel