Zamfara: Kotu ta tsare tsohon kwamishinan Yari da aka gurfanar da laifin satar Shanu da garkuwa da mutane

Zamfara: Kotu ta tsare tsohon kwamishinan Yari da aka gurfanar da laifin satar Shanu da garkuwa da mutane

A ranar Juma'a ne wata babbar kotun Sharia da ke zamanta a Gusau, jihar Zafara, ta bayar da umarnin a tsare tsohon kwamishinan kananan hukumomin jihar Zamfara, Bello Dankande, bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa zarginsa da hannu a satar Shanu da garkuwa da Mutane.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa umarnin da kotu ta bayar a kan Danakande yana zuwa ne a cikin kasa da sa'a 48 da wata kotun jihar ta bayar da umarnin tsare wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Kotun ta bayar da umarnin tsare sakataren yada labarai a kwamitin jam'iyyar APC bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa tuhumarsa da laifin ingiza jama'a da bata suna.

An gurfanar da Dankande ne a gaban kotun mai shari'a, Jastis Hadi Sani, bisa zarginsa da yin garkuwa da wasu mutane biyu da kuma samunsa da hannu a satar Shanu 50 da Tumaki 50.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel