Gwamna Matawalle ya karbe filayen noma da kiwon dabbobi a Zamfara

Gwamna Matawalle ya karbe filayen noma da kiwon dabbobi a Zamfara

Mun samu labari Mai girma Bello Matawalle ya sanar da matakin da gwamnatinsa ta dauka na karbe duka filayen da aka raba domin kafa wuraren kiwon dabbobi tun daga 1999 zuwa yanzu.

Darekta Janar na yada labarai na jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bada wannan sanarwa a Ranar Asabar, 30 ga Watan Nuwamban 2019. Hakan na zuwa ne bayan wasu sababbin kashe-kashe.

Idan ba ku manta ba a cikin ‘yan kwanakin nan, aka kashe akalla mutum 14, haka zalika an jikkata wasu fiye da mutum 10. Wannan ta’adi ya auku ne a Garin karaye da ke Garin Gummi.

Wannan ne karon farko da ‘yan ta’adda su ka sabawa yarjejeniyar sulhun da aka yi da gwamnatin jihar. Wannan ya sa gwamnan Zamfara ya dauki matakin janye filayen noma da ke cikin jihar.

Kamar yadda jawabin da aka fitar a karshen makon nan ya nuna, gwamnan ya ce wannan mataki ya zama dole domin shawo karshen matsanancin rikicin da ake fama da shi a Zamfara.

KU KARANTA: Matar Buhari ta zargi wasu masu mulki da rashin kokari

Gwamnatin Mai girma Bello Matawalle ta nuna cewa kashe-kashen da ake faman yi a jihar, bai rasa nasaba da filayen da aka ware domin kiwon dabbobi da noma a jihar a lokutan baya.

A jawabin da Idris ya fitar, ya bayyana cewa za a sake rabo filayen kiwo a jihar nan ba da dadewa ba. An nada wani kwamiti na musamman da zai yi wannan aiki, ya mikawa gwamnatin rahoto.

“Karbe filayen gona da aka yi zai fara aiki ne ba tare da wata-wata ba. Kuma ana kira ga duk wanda wannan ya shafa, su yi biyayya ga umarnin gwamnati.” Inji Mai girma Gwamnan jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel