Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a wata arangama da Sojoji a Borno

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a wata arangama da Sojoji a Borno

Dakarun yaki da ta’addanci na rundunar Operation Lafiya Dole da Sojojin kasar Chadi sun yi ma mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram jini da majina a wani samame da suka kaddamar a kansu a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba.

Sojojin sun yi artabu da yan ta’addan ne a tsibirin Duguri dake karshen yankin Arewacin jahar Borno tare da taimakon dakarun rundunar Sojan saman Najeriya, inda suka yi ma yan ta’addan kaca kaca duk kuwa da cewa akwai yanayin danshi a yankin.

KU KARANTA: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Sai dai duk da kalubalen da Sojojin suna fuskanta, sai da suka fatattaki yan ta’adda daga garuruwan Njarwa da Duguri, wanda suka kasance manyan mabuyan yan ta’addan, sa’annan suka kwace motocin yakinsu, tare da lalatasu.

Sojojin sun kwace motocin yaki guda hudu bayan sun kashe yan ta’adda 13, tare da kwace bindigu masu baro jirgin sama guda 3, bindigu kirar AK 47 guda 12, alburusai da dama da sauran kayan yaki daban daban.

Sai dai daga bangaren Sojojin, Boko Haram ta jikkata dakaru guda hudu, inda aka kwashe guda biyu zuwa cibiyar kulawa da Sojoji dake kusa da yankin, kuma suna samun sauki, yayin da aka wuce da sauran biyun zuwa babban asibitin Sojoji.

A madadin babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, babban kwamandan yaki na Operatiob Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya jinjina ma Sojojin da suka samu wannan gagarumar nasara duk kalubalen da suka fuskanta.

Haka zalika babban kwamandan ya mika godiyarsa ga rundunar Sojin kasar Chadi bisa gudunmuwar da suke baiwa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, daga nan ya yi kira ga Sojojin dasu jajirce wajen ganin sun kawo karshen Boko Haram gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel