Za a ba wasu Gawurtattun ‘Yan kasuwa 25 sandar girman NPOM

Za a ba wasu Gawurtattun ‘Yan kasuwa 25 sandar girman NPOM

Mutane 26 ne za a mikawa lambar yabo yau Alhamis a Najeriya. Kamar yadda mu ka samu labari daga gidan talabijin na Channels TV, daga cikin wadannan mutane akwai Aliko Dangote.

Bayan shugaban kamfanin na Dangote, akwai sauran manyan kasuwan kasar da masu taimakon al’umma irinsu Shugaban bankin UBA, Tony Elumelu, mai gidauniyar nan ta Tony Elumelu.

Saura sun hada da John Momoh anda ya ke da kamfanin Channels TV. Bayan wadannan mutane masu cin gashin kansu, akwai kungiyoyi bakwai da za su tashi da wannan lamba ta girma.

Gwamnatin tarayya ta ma’aikatar kwadago ce ta shirya bikin bada lambar girma ga wadanda su ke kokari wajen bunkasa karfin kasar. Daga ciki akwai wadannan ‘yan kasuwa da hannun jari.

Aliko Dangote mai kamfanin Dangote shi ne Mai kudin Najeriya da kaf Nahiyar Afrika. Dangote wanda aka taba ba lambar GCON, ‘dan kasuwa ne da wanda ya ke da dubunnan ma’aikata.

KU KARANTA: Za a biya N10, 000 domin a saurari Zahra Buhari - Indimi

Tony Elumelu shi ne shugaban daya daga cikin bankin UBA mai ma’aikata 30,000. Sannan shi ne mai kamfanin Heirs Holding da Transcorp. A baya an karrama shi da lambar CON da MFR.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Oba Otudeko CFR ya na cikin wadanda za a ba wannan kyauta. Otudeko babban ‘dan kasuwa ne kuma shi ne ke da kamfanin abincin Honey Well.

Da yake jawabi a Ranar 26 ga Nuwamban 2019, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa dalilin bada kyaututtukan shi ne zaburar da mutane su kara kokari wajen taimakawa Najeriya.

Dr. Ngige ya ce gwamnati ta san irin kwazon wadannan mutane da tasirin aikinsu wajen cika burin da ta sa gaba. Ngige ya ce: “Babu kasar da za ta kai ga ci a Duniya ba tare da karfin tattali ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel