Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna

Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna

- Hukumar raya birane da safayo ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta rushe gidaje 300 a wasu unguwannin garin Kaduna

- Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun bayyana cewa jami'an KASUPDA sun rushe gidajen ne tsakar dare

- An gano cewa, da yawa daga cikin gidajen an rushe wani sassa ne nasu inda wasu kuma katanga kadai aka sauke musu

Hankulan mazauna birnin Kaduna sun tashi, sakamakon rushe sama da gidaje 300 da cibiyar habaka birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta yi. Wasu gidajen da aka rushe din ana kan ginasu ne, wasu daga ciki kuma an kammala har an tare.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, Yusuf Zomo, mai gidan haya a yankin, yayi magana a madadin wadanda abun ya shafa. Yace jami’an KASUPDA din sun iso yankin ne a ranar Juma’a, wajen karfe 12 na dare inda suka dinga rushe gidajen.

DUBA WANNAN: Kauye: Gwamnatin Zamfara ta dauki alkawarin kara wa 'yan bautar kasa alawus

An gano cewa, da yawa daga cikin gidajen an rushe wani sassa ne nasu inda wasu kuma katanga kadai aka sauke musu.

Zomo ya ce jami’an KASUPDA din, wadanda suka samu rakiyar jami’an tsaro rike da bindigogi, sun iso yankunan ne da motocin ture gini.

Kamar yadda Zomo ya sanar, wuraren da abun ya shafa sun hada da: Babban Saura, Anguwan Waziri, Karji, Tsohon Kamanz da Anguwan Maigyero duk a kan titin Yakowa, Kaduna.

Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Source: Twitter

Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Source: Twitter

Rusau: Hotunan gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Gidajen da KASUPDA ta rushe a Kaduna
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel