Gwamnatin jihar Kano ta kwace tare da rushe wani filin sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da darajarsa ta kai miliyan N250, sannan ta amince da biyansa miliyan N4.5 kacal a matsayin kudin diyya.
Akwai 'yan rigingimu a tsakanin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da sarki Sanusi II, lamarin da yasa gwamnatin Kano a karkashin jagorancin gwamna Ganduje ta kirkiri sabbin masarautu hudu domin rage wa basaraken karfi.
A cikin satin da ya gabata ne wata babbar kotu a Kano a karkashin mai shari'a Usman Na'abba ta soke dokar da ta bawa gwamnatin jihar damar kirkirar sabbin sarakunan yanka 4 masu daraja daya da sarki Sanusi II.
Sai dai, wasu masu nazarin al'amura sun bayyana cewa hukuncin kotun kan iya lalata sauran 'yar kyakyawar alakar da ta rage a tsakanin jagororin biyu.
Wani binciken hadin gwuiwa da jaridun 'Daily Nigerian' da 'Kano Focus' suka gudanar a kan filin da aka rushe, sun gano cewa filin yana kan titin Ibrahim Dabo a cikin birnin Kano kuma an rushe shi ne domin gina gada a shataletalen shagon sayar da maguguna na 'Dangi'.
Jaridun sun bayyana cewa kwamishinan aiyuka, Injiniya Muaz Magaji, shine da kansa ya jagoranci rushe filin a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2015.
Wasu ma'aikatan hukumar kasa da safayo a jihar Kano sun sanar da jaridun cewa sarki Sanusi ya sayi filin mai girman hekta 1.2 a shekarar 2010 a kan kudi miliyan N200, tare da bayyana cewa darajar filin yanzu ta kai miliyan N250m.
Da aka tuntubi shugaban ma'aikatan fadar sarkin Kano, Munir Sanusi, a kan batun ya ce ba zai iya cewa komai a kai ba saboda sarki Sanusi bai bashi damar yin magana a kan lamarin ba.
Sai dai, wata majiya a cikin fadar Kano ta sanar da cewa har yanzu gwamnatin Kano bata biya Sarki Sanusi II ko sisi ba matsayin diyya.
A hirar da wakilan jaridun suka yi da kwamishinan aiyukan, ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Kano ta biya Sarki Sanusi diyyar kudin filin da aikin hanyar ya shafa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng