2023: ‘Dan takarar Arewa za ni marawa baya – Shugaban AFC, Kwande

2023: ‘Dan takarar Arewa za ni marawa baya – Shugaban AFC, Kwande

Mukaddashin shugaban kungiyar Dattawan Arewa ta ACF, Alhaji Musa Liman Kwande, ya ce mutanen Yankin za su zabi mutumin Arewa ne ko a wace jam’iyya ya tsaya takara a zaben 2023.

Musa Liman Kwande ya nuna cewa babu ruwansa da jam’iyya a zabe mai zuwa. Dattijon kasar ya ce wannan shi ne ra’ayin kashin kansa a matsayinsa na ‘Dan kasa kuma mutumin Arewa.

Da ya ke wannan jawabi a Ranar Lahadi, 24 ga Watan Nuwamba, a Garin Lafia ta jihar Nasarawa, shugaban kungiyar ta ACF ya nuna cewa ba ya na magana a madadin kungiyarsa ba ne.

“Mutanen Arewa da aka jarraba su, aka gamsu da su, su yi takarar kowane ofis da kowane ‘dan siyasa daga fadin kasar nan, sannan a ba mutane su fito su kada kuri’arsu ga wanda su ke so.”

KU KARANTA: 2019: Abin da aka yi a Kogi bai yi kama da zabe ba - Kungiya

Kwande ya shaidawa Daily Trust cewa ACF da Takwararta ta NEF su na kokarin kawowa yankin Arewa da fadin kasar cigaba ne kamar sauransu Afenifere da Ohaneze da ke Kudacin kasar.

Alhaji Musa Kwande wanda ke rike da sarautar gargaiyar Baraden-generalismo na kasar Lafia ya yi kira ga daukacin mutanen Arewa su rika zaben ‘yan siyasa masu kishi da kuma nufin cigaba.

“Najeriya ce kasar mu, dole mu hada-kai mu ga ta cigaba duk da banbancin wuraren zamanmu. Ba za mu yi kasa a gwiwa wajen gyara Najeriya ba, domin mu na da arziki da tarin baiwa.”

Dattijon ya ke cewa babu wanda zai gyara Najeriya sai mutanenta. Kwande ya kare jawabinsa da cewa jama’a su daina tada rikicin zabe sannan ‘yan siyasa su rika amincewa da sakamakon zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel