Shehu Sani ya yi magana kan tazarcen Buhari da kudirin Majalisa

Shehu Sani ya yi magana kan tazarcen Buhari da kudirin Majalisa

Fitaccen Sanata a majalisar da ta shude, Shehu Sani, ya yi magana a game da batun sake zarcewan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan mulki da kuma wani kudiri da ke majalisa.

Sanata Shehu Sani ya maida martani bayan da shugaban kasar ya fito wajen taron jam’iyyar APC Ranar Juma’a, ya na tabbatarwa Duniya cewa ba zai sake neman komawa ofis bayan 2023 ba.

Sani ya rubuta: “Sarki ya ce babu batun karin wa’adi a mulki; ka da a samu masu wannan raji da kira a fada, ka da wani a gefen sandar girma ya ce ‘ya kamata (Sarki) ya amsa kiran jama’a’

Bayan jawabin shugaban kasar, Sani ya cigaba da shagube a dandalin sada zumunta na Tuwita ya na mai cewa: “Kuma ka da wani Limami ko Malami ya ce (ga Sarki), ya amsa kiran Ubangiji”

A Ranar Asabar, 23 ga Watan Nuwamba, 2019, tsohon ‘dan majalisar ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita har ya kara da cewa ka da wani ya zo ya na karyar tazarcen yin Ubangiji ne.

KU KARANTA: Sanata ya fito a matsayin Sanata a wasan kwaikwayo

Sanatan ya na yi wa na-kusa da shugaban kasar kashedi: “Sarki ya ce babu karin wa’adi. Ka da a rika jin abubuwa irin su “Ka na na ka, Allah ya na na sa” kuma ka da a ji “Ai haka Ubangiji ya so…”

Haka zalika tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya yi tsokaci a game da kudirin yakar kalaman kiyayya da ke gaban majalisa wanda ya jawo surutu inda ya nemi kowa ya fito da ra’ayinsa a fili.

"Ya kamata duk ‘dan majalisar da bai tare da kudirin yakar kiyayya ko kuma na takawa dandalin sada zumunta burki, ya iya fitowa ya yi magana a gaban majalisa ya bayyana matsayarsa.”

Sani ya kara da: “Wannan gum din da ake yi ko kuma zama jemage, bai dace ba, kuma ragonta ne.” Kwamred ya bada labarin wani Abokinsa da ke sukar marasa goyon bayan wannan kudiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel