Yadda ma'aikacin gidan yari ya lakada wa fursuna duka har sai da ya mutu

Yadda ma'aikacin gidan yari ya lakada wa fursuna duka har sai da ya mutu

'Yan gidan fursuna da ke gidan gyaran hali na karamar hukumar Eket da ke jihar Akwa Ibom, sun fito zanga-zanga a ranar Asabar kan zargin wani ma'aikacin gidan gyaran halin da kisan dan uwansu.

Wata majiya wacce ta bukaci a a boye sunanta, ta zargi cewa ma'aikacin gidan gyaran halin yayi wa dan uwansu mugun dukan da ya yi ajalinsa.

Amma a maida martanin gaggawa da hukumar ta yi, tace dan fursunan ya rasa ransa ne bayan da ya samu matsala wajen numfashi.

'Yan gidan fursunan sun lalata kadarori tare da balla dakuna hudu na gidan. Sun yi kira ga mataimakin shugaban gidan da ya canza musu gida.

An gano cewa,'yan gidan fursunan sun tsere daga gidan amma ma'aikata sun kamasu ta hanyar harbin wasu da raunatasu.

"Dakin shan magani, madafi, wajen aje abinci da wasu sassa na gidan duk an lalatasu," wata majiya tace.

Ya yi bayanin yadda 'yan gidan fursunan suka haka ramuka a kasa wadanda suka taimaka musu wajen tserewa.

DUBA WANNAN: Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

An gano cewa, jami'an tsaron gidan rike da manyan makamai ne suka zagaye asibitin da aka kwantar da fursunoni da suka jigata.

A yayin maida martani a kan lamarin, jami'in hulda da jama'a na gidan yarin, Josiah Ogabajie, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce, zangar-zangar 'yan gidan fursunan ta biyo bayan mutuwar dan uwansu ne da ya rasu sakamakon rashin lafiya a ranar Alhamis.

Ogbajie, wanda ya musanta zargin cewa ma'aikacinsu ne ya kashe dan fursunan, yace an gaggauta kama hanyar kaishi asibiti bayan da aka lura ciwonsa ya ta'azzaar. Amma ana kan hanya ya rasu.

Kamar yadda yace, 'yan uwansa na gidan fursunan sun zargi cewa ba a kula dashi kamar yadda ya dace bane, shiyasa suka fito zanga-zangar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel