Wata sabuwa: Annabi ya halatta jin kade-kade da wake-wake - Inji Limamin Harami

Wata sabuwa: Annabi ya halatta jin kade-kade da wake-wake - Inji Limamin Harami

Tsohon Limamin Masallacin Harami Mai Alfarma dake Makka ya ce an yi raye-raye da kaɗe-kaɗe a zamanin Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, a kamar yadda jaridar The New Arab ta ruwaito

Sheikh Adil Al-Kalbani, wanda a yanzu yake aiki a wani masallaci a Riyad, babban birnin Saudiyya, ya jawo wani hadisi a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Saudiyya mai suna SBC, wanda ke cewa matar Annabi, Sayyidatuna Aisha, ta yi waƙa ga maƙobtanta guda biyu.

Hadisai dai su ne suka taskace irin ayyukan da Annabi Muhammad ya yi, kuma wani tushe ne mai ƙarfi na Shari’ar Muslunci.

Sheikh Al-Kalbani ya kuma jawo wani hadisi wanda Annabi Muhammad ya hango wata mata sannan ya tamabayi Aisha ko ta san ta. Lokacin da Aisha ta ce ba ta san ta ba, sai Annabi ya ce: ”Ita ce Qena, zabiyar zamaninmu”, sannan Aisha ta roƙe ta ko za ta so ta rera mata waƙa.

Sheikh Al-Kalbani ya kuma ambaci cewa Annabi ya je wani ɗaurin aure inda mata suka yi waƙa kuma suka buga mandiri.

Musulmi masu ra’ayin mazan jiya, wanda shi ne ra’ayin da ake yi a Saudiyya suna da fahimtar cewa kiɗa haram ne.

Sheikh Al-Kalbani ya bada fatawar da ta bada damar yin waƙa a baya, amma ya janye fatawar a shekarar 2010.

“Bayan shiga tsakani da tattaunawa da mutanen da nake ganin girman su kamar Ministan Harkokin Addinin Musulunci, na gamsu cewa waƙar da na bada fatawar a yi babu ita a yanzu”, ya bayyana haka a wata tattaunawa da jaridar Al-Hayat.

KU KARANTA: Rainin wayo: Bayan an kama shi da laifin lalata da 'yar gidan matarshi mai shekara biyu, ya ce wai ya zaci matarshi ce

Sheikh Kalbani shi ne baƙar fata na farko da ya yi limanci a Makka, kamar yadda tarihinsa da jaridar New York Times ta bayar ya nuna.

“Wasu mutane a ƙasar nan suna so kowa ya yi halayya kamar zamanin Sahabbai”, Sheikh Kalbani ya faɗi haka a tarihin da jaridar ta wallafa a shekarar 2009.

“Wannan ba shi ne tunanina ba. Za ka iya koya daga mutumin da ke son yin suka don bada wata fahimtar ta daban”, ya ƙara da haka.

A lokacin da aka naɗa shi a matsayin Limamin Masallacin Harami Mai Alfarma dake Makka, mutane sun kalli naɗin a matsayin wani ƙoƙarin da Sarkin Saudiyya, Sarki Abdullah ke yi na sassauta tsattsaurar ra’ayin masarautar.

Shekaru 10 bayan nan, Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya fara taka muhimmiyar rawa a masarautar, ana sassauta dokokin da suka hana mata da baƙi ‘yan ƙasashen waje sakat a hankali a hankali.

Kalaman na Sheikh Kalbani sun zo ne a daidai lokacin da Riyad ke ci gaba da ɗaukar “ra’ayi tsaka-tsaki” na Musulunci da gwamnati ke fassarawa, koda yake dai mutane da dama sun ƙalubalanci wannan ra’ayi.

Masu suka dai suna ganin gyare-gyaren da Yariman ke yi ba su da ma’ana matuƙar dai maza na ci gaba da kula da mata.

A wani faifan bidiyo da jaridar Saudiyya, Arab News ta wallafa, Sheikh Kalbani ya fito da matsayin cewa ba buƙatar a sa shinge a raba tsakanin mata da maza a yayin salla a Masallacin Harami, saboda ba a yi haka ba a zamanin Annabi.

Sheikh Kalbani ya yi jayayyar cewa mata a yau suna fuskantar takurawa da sake ‘nesanta su da al’umma” fiye da lokacin Annabi Muhammad.

Malamin ya ce duk da ra’ayinsa na baya game da malaman Shi’a da ya bayyana a matsayin waɗanda fahimtarsu ta saɓa da Musulunci, ya canza tunaninsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel