Allahu Akbar: Dan wasan kasar Amurka Van Damme ya shawarci mutane suyi koyi da abinda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar

Allahu Akbar: Dan wasan kasar Amurka Van Damme ya shawarci mutane suyi koyi da abinda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar

- Musulunci addini ne na gaskiya amma ana shigarshi ne da shiryarwar Allah

- Wata jarida ta yi wa sanannen dan wasan fina-finan Hollywood na kasar Amurka tambayoyi a kan abinci da kiwon lafiya

- Ya bayyana cewa, komai a kan kiwon lafiya na cikin koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W) saboda hikimar da yake da ita

Musulunci addini ne na gaskiya. Allah ya saukar mana da Al-Qur’ani a matsayin shiriya don mu bi shi. Allah ya turo mana Annabi Muhammad a matsayin ma’aiki ne. Madubin dubawa ne garemu kuma an umarcemu da mu bi sunnarshi. Ba Musulmai kadai ke bin koyarwar Annabin rahamar ba.

Kwanan nan aka tambayi dan wasan fina-finan kasar Amurkan nan na masana'antar Hollywood, Jean-Claude Van Damme a kan yadda ake cin abinci kamar yadda kiwon lafiya ya tanadar, sai ya bada amsa da: “Annabi Muhammad ne ke da amsar, don ya koyar da yadda za a ci abinci tare da abubuwan da yakamata matasa su ci masu kara lafiya.”

Ya kara yin bayani akan yanayin jinin mutum da sauran abubuwan da suka shafi kiwon lafiya. Ya ce: “Cin abinci mai kyau, barci mai kyau. Zaka iya cin abinci da nama ko a sati sau daya ne. Idan nace nama, ba ina nufin nama mai yawa bane. Ganyayyaki da sauran abincin larabawa masu gina jiki.”

KU KARANTA: Mijina da kwaroron roba yake kwanciya dani shine yasa nake neman wadanda za su gamsar dani a titi - Inji wata matar aure

“Ka duba lokacin Annabi Muhammad. Musulmai na cin gurasa ne da kuma kayan lambu. Annabi Muhammad ya san abinda ya dace da kowanne zamani kuma mai gina jiki. Don haka ni bana son kuna tambayata, ku bincika daga koyarwar shi."

"A cikin koyarwar shi akwai tarin hikima da dabarun da zasu dace da zamani," in ji Van Damme.

Muna yi mishi addu'ar Allah ya shiryar da shi zuwa addinin Musulunci. Ameen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel