Kaduna: Aisha tayi yunkurin yankewa Abdullahi mazakuta bayan yace ba zai aureta ba

Kaduna: Aisha tayi yunkurin yankewa Abdullahi mazakuta bayan yace ba zai aureta ba

- Jami’an hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, sun cafke wata matashiya mai shekaru 23 a kan zargin yunkurin yankewa saurayinta mazakuta

- Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Soba, inda kowa ya san Aisha da Abdullahi a matsayin masoyan juna

- Ta sanar da hukumar ‘yan sandan cewa, ya maidata kamar matarsa da alkawarin zai aureta kuma ta kori duka manemanta saboda shi

Jami’an ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama wata matashiya mai shekaru 23 a duniya a kan zarginta da sokawa masoyinta mai shekaru 34 wuka.

An gano cewa, sunan wacce ake zargin Aisha Abdullahi kuma ta yi yunkurin ba saurayin nata mai suna Musa Abdullahi guba kafin ta hareshi da wukar a karamar hukumar Soba.

Abdullahi ma’aikacin lafiya ne a Soba kuma yana da mata daya da yara uku. Ya dade yana soyayya da Aisha tare da mata alkawarin aure. Amma kwatsam rana daya ya zo yace mata ya fasa.

Aisha Abdullahi ta ba saurayinnata guba a cikin wani abin sha, amma masoyinnata ya zargeta, saboda haka bai karba ba.

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Oktoba, kowa dai ya san Aisha da Abdullahi masoyan juna ne. Aisha ta samo karti wadanda suka bankare mata Abdullahi bayan da suka tare shi, ta soka mishi wuka a wurare da yawa a jikinshi har ta yi kokarin yanke masa mazakuta.

KU KARANTA: Jerin kasashen da suka fi ko ina hadari a duniya a shekarar 2020

Tuni aka hanzarta kai Abdullahi wani asibiti da ke Soba inda a ka mishi aiki a mazakutarshi. Yanzu haka dai an maida shi wani aisbiti da ke Zaria don kara yi mishi aiki a gaban nashi.

Wakilin jaridar Aminiya ya gano cewa, Abdullahi ya samu raunika a fuska, kai, hanci, hannu da kuma mazakutarshi da ta yi yunkurin tsinkewa

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya ce an fara bincike a kan lamarin. Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa Aisha ta ce, ya fara mu’amala da ita kamar matarshi amma sai daga baya ya ce mata ya fasa aurenta. Ana jira Abdullahi ya wartsake kafin a mika fayel dinsu zuwa babbar hedkwatar binciken ‘yan sandan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel