Budurwa ta auri saurayinta a ranar da ta fara haduwa da shi

Budurwa ta auri saurayinta a ranar da ta fara haduwa da shi

- Jaruma Padita Agu ta bada labarin yadda suka yi aure da tsohon mijinta a ranar da suka fara haduwa

- Tsohon mijin nata ya ganta ne a gidan kawarta , duk da ita bata lura da shi ba, ya bayyana ra'ayinsa a kanta ta hannun kawarta

- Bayan doguwar soyayyar waya, sun amince da yin aure ranar da zasuyi haduwar farko

Jaruma Padita Agu ta bada labarinta mai cike da ban mamaki, labari ne na yadda aurenta na shekaru 3 ya mutu.

A wani bidiyo da ta sanya a shafinta na YouTube, Padita ta bada labarin yadda ta auri tsohon mijinta a ranar da suka fara haduwa, bayan sun yi doguwar soyayya ta waya.

Kamar yadda ta ce, ta hadu da tsohon mijinta ne, a gidan kawarta. Bayan barin gidan kawartan sai ta kirata da cewa, mutumin da ta gani a gidanta yana da ra'ayinta kuma yana bukatar lambar wayarta.

Padita ta bayyana cewa a lokacin ta na soyayya don haka ne ta ki amincewa da tayin, amma kawarta ta takurata sosai inda daga baya ta aminta da bukatar kawartata. A lokacin da suka fara yin magana da mutumin yana kasar waje.

Bayan doguwar soyayya ta waya, sai suka fara zancen aure. A cikin daya daga cikin hirarrakinsu ne, tace, ya fada mata wata magana da har yau take da ta sani.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda aka kama wasu matasa guda hudu suna yiwa wata yarinya fyade ta karfin tsiya

"Saurayin ya bukaci mu yi aure ne ranar da zamu fara haduwa. Duk da bana tuna fuskarsa, zata yuwu shi ya ganni sosai ranar da muka hadu a gidan kawata, ko kuma a fina-finai na."

Yace mu shirya aure kawai, mu hadu a kotun ranar auren. Duk da nayi ta tunanin me dangina zasu ce? Me zan ce musu? Sai yace ba sai mun sanar da danginmu ba.

A zancen da muka yi ni da shi kuwa shine, duk ranar da muka hadu muka ga bamu yi wa juna ba, zamu iya hakura da juna, babu wanda ya sani. Kawai sai nayi tunanin babu cutarwa a lamarin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel