Tashin hankali: Jirgin sama ya turnuke da hayaki jim kadan da saukarsa a Masar

Tashin hankali: Jirgin sama ya turnuke da hayaki jim kadan da saukarsa a Masar

- Jirgi sama dauke da fasinjoji 196 ya turnuke da hayaki bayan ya sauka a filin jirgin sama a Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar

- Lamarin ya afku ne a lokacin da jirgin ya koma wajen tsayuwarsa sannan fika-fikinsa na hagu ya kama dunkulallen wuta

- Ma’aikatan filin jirgin sun yi gaggawan kashe wutar ba tare da amfani da wasu kayayyaki na musamman ba

Wani jirgin sama mai lamba 737-800 dauke da fasinjoji 196 ya turnuke da hayaki bayan ya sauka a filin jirgin sama a Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar.

Jirgin na (UR-SQH), da ke gudanar da PQ7153 daga Zaporizhia a ranar 9 ga watan Nuwamba, ya koma wajen fakin dinsa bayan ya sauka, inda ya turnuke da hayaki ta bangarensa na hagu jim kadan bayan ya tsaya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa na’urar CCTV daga fili jirgin saman ya nuno lokacin da jirgin ya tsaya sannan fika-fikinsa na hagu ya kama dunkulallen wuta.

Ma’aikatan filin jirgin sun yi gaggawan kashe wutar ba tare da amfani da wasu kayayyaki na musamman ba.

Babu mutum ko guda cikin fasinjoji 189 da ma’aikatan jirgin da ya samu rauni.

KU KARANTA KUMA: Mijin mace 1: Ba zan taba yiwa matata Maimunatu kishiya ba – Ali Nuhu

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar kiyaye hadura wato FRSC shiyar jihar Ogun ta sanar da mumunan hadarin da ya auku da babban titin Legas zuwa Ibadan da yammacin nan inda aka rashin rayuka 13.

Hukumar ta bayyana cewa hadarin ya faru ne garin Ogere, jihar Ogun kuma mutane 37 ke cikin motocin da ya shafa.

Hadarin ya auku ne tsakanin kananan motoci biyu da babbar mota tirela daya. Hakazalika mutane goma sun samu raunuka iri-iri kuma an garzaya da su asibitin Victory dake Ogere, jihar Ogun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel