Mijin mace 1: Ba zan taba yiwa matata Maimunatu kishiya ba – Ali Nuhu

Mijin mace 1: Ba zan taba yiwa matata Maimunatu kishiya ba – Ali Nuhu

- Shararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana cewa mata guda daya tal ya ke da burin mallaka a rayuwarsa kuma ita ce matarsa Maimuatu

- Har ila yau Ali ya ce yara hudu ya ke burin haifa, sai dai ya ce mai sa tanadin da Allah ya yi masa ba

- Ali ya ce bai da yan mata a masana'antar sai dai 'ya'ya, sanan cewa ya fi kusa da darakta Hafiz Bello fiye da kowa a dandalin

Fitaccen jarumin nan na Kannywood wanda ake yyiwa lakabi da sarki mai sangaya, Ali Nuhu ya bayyana cewa mata guda daya tal ya ke da burin mallaka a rayuwarsa.

A hira da ya yi da shafin BBC Hausa, jarumin ya jaddada cewa daga Maimuna babu kari domin ita daya ta ishe shi zaman gidan duniya.

Kan yawan yayan da yake burin mallaka a rayuwarsa, Ali ya ce yara hudu kacal yake son ya Haifa, amma kuma Allah ne ya baiwa kansa sani.

Da aka tambayi jarumin game da yawa yan matasan na Kannywood, Ali ya bayyana cewa bashi da yan mata sai dai ‘ya’ya, inda ya bayyana sunayen yaran nasa a matsayin Hadiza Gabon, Maryam Yahaya da sauran su.

kan shawarar da aka fi bashi a rayuwa; Ali ya bayyana cewa a fi bashi shawara ne kan abunda ya shafi harkokin sana’arsa, da kuma dangantakarsa da mutane

har ila yau jarumin ya bayyana Hafiz Bello a matsayin a hannun damarsa a masana’antar duk da cewar ba kasafai ake ganinsu tare ba. Ya ce hakan yyaamo asali ne tun zamanin yarantarsu domin a cewarsa tare suka taso har girmansu.

Ya kuma bayyana cewa darakta Hafiz shine mutumin da basu taba samun tangarda da shi ba a Kannywood.

KU KARANTA KUMA: Dankari: Yadda ma’aikacin banki ya hada kai da wasu suka yashe wani kwastama bayan sun yi tunanin ya mutu

Baya ga harkar fim, jarumin ya bayyana cewa yana harkar ado da kwaliyya wato fashion design da kuma kiwon kaji.

Game da inda ya ke uin ganin kansa nan da shekaru 10 masu zuwa, Ali ya ce a lokacin yana fata yin ritaya sannan ya ga kansa cikin yaransa, watakil ma harda jika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng