Mayakan Boko Haram 16 tare da matansu sun mika wuya ga rundunar soji

Mayakan Boko Haram 16 tare da matansu sun mika wuya ga rundunar soji

Wasu mutane 16 da suka tabbatar da cewa su mambobin kungiyar Boko Haram ne da takwararta ISWAP sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya a jihar Borno, kamar yadda jaridar Tribune ta rawaito.

An alakanta mika wuyan mayakan da matsin lambar da suke fuskanta daga dakarun soji, wadanda ke cigaba da kaddamar da hare-hare a sansani da maboyar mambobin kungiyoyin ta'addanci da ke yankin arewa maso gaba.

Shugaban sashen yada labarai na rundunar soji, Kanal Aminu Iliyasu, shine wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabai da ya fitar ranar Jama'a.

Kanal Iliyasu ya bayyana cewa dakarun soji sun kashe mayakan kungiyoyin da yawa a karkashin atisayen 'Operation Lafiya Dole'.

"Mun damka mayakan da suka mika ga wuya ga rundunar soji ta 3 a garin Gambamboru Ngala dake kuryar arewacin jihar Borno.

DUBA WANNAN: Manyan masu kudin duniya 5 da basu kammala karatun sakandire ba

"Sun tabbatar mana da cewa suna da hannu a hare-haren da aka kai a kan dakarun soji da farar hula a sassan jihar Borno. Mun dauki bayanansu kafin mu mika su hannun bataliyar soji ta uku," a cewar jawabin.

Kanal Aminu ya lissafa sunayen mayakan da suka mika wuyan, kamar haka; Ibrahim Bunu, Abba Sale, Baba Lamba Alhaji, Bukar Isa, Bukar Ali, Rawa Abba Gana, Mustapha Abatcha, Umar Abubakar, Hassan Bukar, Malan Abatcha Ali, Abba Umar Abatcha, Hussaini Babagana, Idris Mohammed da Umar Abba Bayoma.

Mayakan Boko Haram 16 tare da matansu sun mika wuya ga rundunar soji
Mayakan Boko Haram 16 sun mika wuya ga rundunar soji
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel