Dan sanda ya kashe mutum a bikin da gwamna ya halatta

Dan sanda ya kashe mutum a bikin da gwamna ya halatta

Ana zargin wani jami'in dan sanda a Akwa Ibom da kashe wani mutum har lahira a wani biki da gwamnan jihar, Udom Emmanuel ya samu halarta.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Ikot Ukab, karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar Akwa Ibom. Har yanzu dai ba a san dalilin kisan mutumin mai suna Godwin Thomas ba.

Mai magana da yawun 'yan sandar jihar, Odiko MacDon ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma'a amma ya ce har yanzu ba a gano dan sandan da yayi aika-aikar ba.

"Binciken mu na farko ya nuna cewa, jami'in tsaron gidan gwamnati da ke wajen baya gurin a yain da lamarin ya faru," kamar yadda SP MacDon ya sanar.

DUBA WANNAN: 2023: Matasan Ohanaeze Ndigbo sunyi muhimmin kira ga Atiku

"Akwai jami'an tsaro daga jihar da kuma jihohin da ke da makwaftaka da jihar don tsaro a wajen bikin," in ji mai magana da yawun 'yan sandan.

"A yayin da har yanzu ba a gano wanda yayi mummunan aikin ba, kwamishinan 'yan sandan jihar, Zaki Ahmed ya bada umarnin a tsananta bincike ta yanda za a hanzarta gano wanda yayi laifin don a gurfanar dashi," in ji shi.

Gidan gwamnatin jihar Akwa Ibom a ranar Juma'a ta ce, gwamnan ya matukar fusata da kisan Mr Thomas.

Wata takarda da ta fito daga kwamishinan yada labarai na jihar, Charles Udoh, ya kwatanta kisan da "abun alhini ana tsaka da murna".

Kwamishinan yace, gwamnan ya bada umarni ga jami'an tsaro da su nemo tare da hukunta wanda yayi kisan.

"A yayin alhinin da mika ta'aziyya ga iyalan wanda aka kashen, gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnatinsa zata cigaba da tsare rayuka da dukiyoyin da ke jiharsa," Udoh yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel