Yanzu Yanzu: Gobara ta sake tashi a wani ginin Lagas

Yanzu Yanzu: Gobara ta sake tashi a wani ginin Lagas

- Wani gini a yankin Ebute Metta da ke birnin Lagas ya kama gobara

- Hakan na faruwa ne kimanin sa'o'i 48 bayan wata gobara ta afku a yankin Balogun, babbar kasuwar jihar

- Alamu sun nuna cewa gobarar ta kama ne ba da wasa ba, domin an gano hayaki na tashi ba da wasa ba

Wani gini a yankin Ebute Metta da ke birnin Lagas ya kama gobara kimanin sa'o'i 48 bayan wata gobara ta afku a yankin Balogun.

Hotunan afkuwar lamarin ya nuna cewa gobarar ta kama ne ba da wasa ba, domin an gano hayaki na tashi ba da wasa ba.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken jawabi daga mahukunta a jihar akan abunda ya haddasa faruwar gobarar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yanzu Yanzu: Gobara ta sake tashi a wani ginin Lagas
Gobara ta sake tashi a wani ginin Lagas
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Yan daba sun shigo Kogi gabannin zaben Gwamna – PDP ta yi zargi

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labarin kuma, mun ji cewa hankula sun tashi jiya yayin da jirgin sama mai lamba rijista JQ2324 da ya tashi daga Legas zuwa Abuja ya fara hayaki a sama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa, jirgin na kamfanin Azman na dauke da fasinjoji 120 ne kuma dole ce tasa ya koma filin sauka da tashin jirage na Murtala Muhammed dake Legas.

Wata fasinja mace ce aka ce ta shiga bayin jirgin inda ta sha shisha. Hakan kuwa ya kawo gobara a bayin jirgin wanda ya kawo tashin hankula.

Tuni aka cafke budurwar kuma aka mikata ga jami'an 'yan sanda. Matukin jirgin ya bukaci da a kara duba jirgin bayan saukarsu ko zasu iya kara tashi.

A cikin fasinjojin da ke jirgin harda mamallakin kamfanin Payporte, Eyo Bassey.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng