Kai duniya: Yadda dan shekara 15 ya dunga luwadi da yaro dan shekara 6 a Kaduna

Kai duniya: Yadda dan shekara 15 ya dunga luwadi da yaro dan shekara 6 a Kaduna

- An samu matashi dan shekara 15 da aikata luwadi da karamin yaro dan shekara shida a jihar Kaduna

- Malamin yaron ne ya hankaltar da mahaifinsa bayan sun gano lamarin sakamakon rashin dawowa da aji da wuri da yaron baya yi idan aka tafi hutun cin abinci

- A yanzu haka yana samun kulawar likita a cibiyar kula da wadanda aka ci zarafinsu na asibitin Gambo Sawaba tare da matashin da ke cin zarafin nasa

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a yanzu haka wani yaro dan shekara shida na karkashin kulawar likita a cibiyar kula da wadanda aka ci zarafinsu na asibitin Gambo Sawaba, Zaria, jihar Kaduna bayan wani matashi dan shekara 15 ya yi luwadi dashi akai-akai.

Mahafin yaron wanda ya ce malamin dan nasa ne ya hankaltar dashi game da lamarin ne ya kai shi cibiyar.

“Sun ce a koda yaushe yaron kan dawo aji cikin kurarren lokaci idan aka tafi hutun cin abinci sannan idan aka tambaye shi inda ya je sai ya bayar da amsar cewa ya je ya hadu da wanda ke cin zarafin nasa ne. Da aka cigaba da tambayarsa, sai ya fada masu cewa matashin da ke cin zarafinsa ya nemi ya cire wandonsa sannan ya yi luwadi da shi,” inji shi.

Da take tabbatar da lamarin ga manema labaai, manajar cibiyar, Amina Umar Faruq tace binciken likitoci ya nuna cewa anyi luwadi da yaron ta duburansa.

KU KARANTA KUMA: Likitocin jahar Kaduna za su tsunduma yajin aiki saboda rashin jituwa da gwamnati

“Bayan binciken mu, mun gano cewa an yi luwadi da yaron ta duburansa. A yanzu yana karkashin kulawar likita da kuma kokarin gyara shi. Yan sanda sun kuma kawo mana matashin da ke lalata dashi sannan ya amsa cewa shima wani ya yi lalata ashi inda ya gaza bayyana sunansa, a yanzu shima yana samu kulawa,” ta fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN).

Umar-Faruq ta kara da cewa a yanzu haka yan sanda na bincike kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel