Wata mata ta kashe jaririn da ta haifa a Kano

Wata mata ta kashe jaririn da ta haifa a Kano

- 'Yan sintiri a unguwar Kawon Arewa a garin Kano sun kama wata mata da ake zargin ta kashe jaririn da ta haifa

- Matar mai suna Aisha Muhammad ta ce ba ita ta kashe jaririn ba, kawai kwanansa ya kare

- Mahaifiyar Aisha ta tabbatar wa da Freedom Radiyo cewa ba diyarta ce ta kashe jaririn ba, tare da rokon a rufe maganar a wurin

Freedom Radio ta wallafa rahoton cewa jami'a sintiri a unguwar Kawo da ke cikin birnin Kano sunsamu nasarar cafke wata mata mai suna Aisha Muhammad bisa zarginta da hallaka jaririn da ta haifa a cikinta.

A cewar rahoton, wata matashiya ce ta fara tona asirin Aisha yayin da ta iske gawar jaririn bayan ta shiga gidan da matar ta haihu, ita kuma ta kwarmata labarin har ta kai ga jami'an sintirin unguwar sun shigo cikin lamarin.

Amma a nata bangaren, Aisha ta bayyana wa wakilin gidan Radiyon Freedom, Aminu Abdu Baka Noma, cewa bata kashe jaririn ba duk da kasancewar ta haife shi ne ba tare da aure ba, kawai karar kwana ce da kaddara suka yi sanadin mutuwarsa.

DUBA WANNAN: Wata mata ta shake 'ya'yan cikinta 2 har lahira bayan sun ki cin abincin da ta zuba wa guba

Mahaifiyar Aisha ta shaida wa Freedom Radio cewa diyarta bata kashe jaririn da ta haifa ba, amma tana rokon a kashe maganar a wurin, saboda, a cewarta, wani makwabcinsu ne ya ci amanarsu ya dirka wa diyarasu ciki.

Mallam Shehu Adamu, sakataren ‘yan sintiri na yankin Kawo ta Arewa, ya bayyana cewa basu bata lokaci ba wajen zuwa gidan su Aisha bayan samun labarin abinda ake faruwa, inda suka taho da yarinyar da mahaifiyarta da kuma gawar jaririn da ake zargin kashe shi Aisha ta yi.

Sakataren ya kara da cewa zasu mika Aisha da Mahaifiyarta ga jami'an tsaro domin su zurfafa bincike a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel