Toh fah: CBN na yunkurin dawo da bashin N36bn daga manoma a arewa maso gabas

Toh fah: CBN na yunkurin dawo da bashin N36bn daga manoma a arewa maso gabas

Babban bankin Najeriya (CBN) ya tanadi wata runduna a dukkanin kananan hukumomi da ke yankin arewa maso gabas domin dawo da bashin naira biliyan 36 da aka ba manoma.

An bayar da bashin ne ga manoma domin bunkasa ayyukansu ta hannun kungiyar Northeast Commodity Association (NECAS) duk a cikin shirin bayar da rance na gwamnatin tarayya.

Da yake kaddamar da kwamitin na kananan hukumomi 27 dake jihar Borno a Maiduguri a jiya Litinin, 4 ga watan Nuwamba, Shugaban kungiyar NECAS na kasa, Sadiq Daware, ya tuna cewa kungiyar ta sanar da manoman da suka amfana daga shirin a jihar cewa kayayyakin da aka rarraba masu bashi ne.

Daware yace kungiyar NECAS ta yi nasarar samun bashin naira biliyan 36 daga bankin CBN akan kayayyaki shida da suka hada da shinkafa, masara, dawa, waken suya, ridi da auduga don manoma a yankin arewa maso gabas.

Ya bayyana ceewa manoman Gombe ne suka samu kaso mafi yawa na bashin saboda sun shuka dukkanin kayayyakin guda shida yayinda manoma 3,722 a jihar Borno suka samu mafi karancin bashin saboda sun dukufa a shukar shinkafa ne kawai.

Ya yi fatan cewa za a shigar da manoma a jihar Borno wadanda za su yi amfani da damar shuka amfanin gona daban-daban cikin shirin a badi.

Ya ce an tsara manufar shirin sosai ta yadda babu wani manomi da zai yi asara koda kuwa an samu lamari na fari.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya roki yan jarida da su daina bata sunan dakarun sojoji wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma

Da yake magana a taron, jami’in cigaban kudi na CBN, reshen Maiduguri, Mahmud Nyako, ya ce biyan bashin ya babbanta daga kaya zuwa kaya.

Nyako ya bayyana cewa za a hukunta wadanda suka saba alkawari ba tare da dalili ba. Amma y ace manoman da suka fuskanci annoba na fari toh su kai rahoton lamarin domin su samu damar cin moriyar shirin da CBN ya tanadar akan irin wannan asara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel