Bidiyo: Yadda aka kama wata fitsararriyar Balarabiya 'yar kasar Saudiyya tana rawar iskanci da Hijabi cikin bainar jama'a

Bidiyo: Yadda aka kama wata fitsararriyar Balarabiya 'yar kasar Saudiyya tana rawar iskanci da Hijabi cikin bainar jama'a

- An kama wata fitsararriyar budurwa 'yar kasar Saudiyya tana rawar iskanci da Hijabi a cikin bainar jama'a

- Budurwar dai an nuno ta a cikin wani sabon bidiyo tana ta rawa ta fitsara sanye da hijabi da nikabi a fuskarta

- Wannan dai duk ya biyo bayan irin canje-canje da kasar ta Saudiyya ke kawowa domin ganin an samu cigaba na zamani a kasar

Kamar yadda kasar Saudiyya take ta kawo sauye-sauye domin kawo cigaba a kasar, yanzu haka dai abubuwa da dama sun fara canjawa. Wani kamfani na bincike da yada labarai na kasar Saudiyya ya bayyana cewa kasar Saudiyyar ta bada umarnin kama wata budurwa da aka kama tana rawar iskanci a cikin Hijabi.

Wannan lamari dai ya faru a birnin Riyadh, a wani waje da maza da mata ke haduwa domin holewa. A yadda rahoton ya bayyana, budurwar tana sanye da wata bakar Abaya ne. Bidiyon ta ya nuna yadda take rawa ta iskanci wanda ya jawo hankalin mutane da dama.

KU KARANTA: An samu Jami'a ta farko a Najeriya da za ta fara yiwa saurayi da budurwa bulala idan aka kama su suna soyayya

Mutane suna ta mamaki ganin yadda irin wannan bidiyo ya fito daga kasar Saudiyya, budurwa na rawa irin wannan a tsakiyar jama'a, kowa dai a wajen ya nuna alamun cewa yana jin dadin wannan rawa da take yi, domin kuwa babu wanda aka nuno a bidiyon da yake kokarin tsayar da ita daga rawar da take yi.

Wasu mutane sunce budurwar ba wai ta ci mutuncin al'adar kasar Saudiyya bane kawai, hatta hijabin da ta sanya shima ta ci mutuncin shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel