Masu bibiyar shafinmu sun ce da wuya farashin shinkafa ya dawo N9000 a Disamba

Masu bibiyar shafinmu sun ce da wuya farashin shinkafa ya dawo N9000 a Disamba

Kawo yanzu mutane da-dama su na kuka a game da yadda shinkafa ta yi tsada a Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin shugaba Buhari ta rufe kan iyakokinta saboda wasu dalilai.

Najeriya ta garkame iyakokin na ta ne domin haramta shigowa da kaya ta kasa. Ana sa rai wannan zai taimakawa Manoman gida ta hanyar bunkasa Manoma da kara masu karfin gwiwa.

Kungiyar Manoma da masu aikin shinkafa sun yi alkawarin cewa babban buhun kilo 50 zai koma N9, 000 kwanan nan. Legit.ng ta tambayi masu bibiyarta ko su na ganin shinkafar za ta rage kudi.

Manoma shinkafar sun ce za a samu karyewar farashi ne muddin aka samu amfanin gona yadda ake sa rai. Wannan ya sa su ka yi wa ‘yan kasar alkawarin saukin shinkafa zuwa Watan Disamba.

Sai dai masu bin labarai a shafinmu su na da ja game da wannan alkawari. Masu bibiyar mu a shafukan sada zumunta ba su yarda cewa shinkafa za ta karye sosai nan da karshen shekara ba.

Da mu ka tambayi masu bin shafin mu na Legit.ng a Tuwita su kada kuri’a game da yadda su ke ganin lamarin, sama da rabinsu sun zabi cewa ba zai yiwu buhun shinkafa ta koma N9000 ba.

KU KARANTA: Neman aiki: Gwamnatin Tarayya ta ba 'Yan Najeriya shawara

Buhun shinkafa zai koma N9, 000 daga yanzu zuwa Watan Disamba idan hatsi su ka yi kyau a gona:

37% Akwai yiwuwar haka

36% Sam! Ba zai yiwu ba.

21% Ba zan iya cewa ba,

6% Oho

Mun koma kan shafin sada zumunta na Facebook inda masu karanta shafin Ingilishi su ka kada kuri'arsu. Shi ma dai a nan ra'ayin na su ya nuna cewa da wuya maganar Manoma ta tabbata.

Zai yiwu shikafar gida ta koma N9, 000 a kan kowane buhun kilo 50 kafin Disamba kamar yadda Manoma su ka yi alkawari.

60% Ba zai yiwu ba!

40% Zai yiwu!

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel