Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya na watanni 5 da suka gabata

Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya na watanni 5 da suka gabata

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar kwadago ta Trade Union Congress (TUC) ta yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta biya bashin karancin albashi na watanni biyar a lokacin da za ta fara biya a wannan watan.

Kungiyar kwadagon wacce ta kasance daga cikin wadanda suka tattauna cikakken aiwatar da sabon karancin albashin a fadin dukkanin matakai tace tana so a biya karancin albashin tun daga lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar sabon albashin a ranar 18 ga watan Afrilu.

An bayyana hakan, a cewar jaridar Premium Times, cikin wani jawabi daga mukaddashin shugaban kungiyar, Anchaver Simon, da sakataren kungiyar, Alade Lawal.

Kungiya ta kara da cewa za ta dauki mataki akan dukkanin ma'aikatar da ta biya kasa sabon karancin albashin da aka tsara.

KU KARANTA KUMA: Fasa kauri: Sojin ruwa sun kama mutum 12, sun kwace buhuhunan shinkafa 708

Ku tuna cewa ministan Kwadago, Chris Ngige yace za a fara biyan sabon karancin albashi ba tare da bata lokaci ba.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadaon akan gyare-gyaren da ya taso daga aiwatar da sabon kaancin albashin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel